Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba a Samun Nasara a Yakin Da Ake Da Sauyin Yanayi a Duniya- Emmanuel Macron


Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya fadawa masu zuba jari a kasashen duniya sama da 200 da shugabannin duniya 50 cewa ba a samun nasara a yakin da ake da sauyin yanayi.

“lokaci yayi da za a ‘dauki matakin gaggawa domin a samu nasarar wannan yaki,” a cewar Macron jiya Talata a wajen taron kolin neman ‘karin kudaden da za a yi amfani da su wajen yakar sauyin yanayi a duniya.

Taron kolin dai na zuwa ne shekaru biyu bayan da kusan kasashe 200 suka amince da yarjejeniyar da aka kulla a birnin Paris kan sauyin yanayi, wadda ta yi kira ga kasashe su takaita samar da gurbatacciyar iska, kuma kasashe masu arziki a duniya su taimakawa kasashe masu tasowa kan illar sauyin yanayi.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ya janye daga yarjejeniyar, yana mai cewa ana kwarar Amurka kuma sauran kasashe ne kadai ke amfana da ita. Yanzu dai Amurka ita kadai ce kasa da ta janye kanta daga yarjejeniyar kasashen duniya kan sauyin yanayi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG