Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Haka Kawai Ake Kikiro Masarautu Ba


Buba Yero Mafindi

Kirkiro masarautu a wannan lokaci da ake fama da tashe tashen da fadar kabilanci nada illa

Batun kirkiro sabbin masarautu tare da tada kafadar wasu kananan sarakuna, da ake zargin gwamnatin jihar Taraba na yunkurin aiwatarwa, ya soma jawo martani daga masana da kuma kungiyoyin fafutuka a jihar, ta Taraba, inda wasu ke danganta lamarin da siyasar 2019.

Wasu majiyoyi dai a gwamnatin jihar na cewa, tuni wannan batu ya kai ga hannun wasu daidaikun ‘yan majalisar dokokin jihar da ake sa ran zasu bada hadin kai.

A wajen wani taron manema labarai a Jalingo fadar jihar, wasu dattawan jihar sun an karar da gwamnatin jihar game da illar dake akwai na yunkurin kirkiro wasu masarautu a yanzu, musamman a wannan lokacin da jihar ke fama da tashe tashen hankula, da kuma fadar kabilanci..

Buba Yero Mafindi, dake daya cikin dattawan jihar, yace ba haka kawai ake kafa masarautu ko daga darajar masarauta ba, inda ya bada misali da masarautar Takum da aka dauki tsawon shekaru ba sarki.

Shima da yake Karin haske, wani lauya kuma kusa a kungiyar cigaban Taraba, watau Taraba Concern Citizens Forum, Barr. M.B Mustapha, yace akwai abun dubawa game da wannan batu.

Don tabbatar da halin da ake ciki a yanzu game da wannan batu, wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz yayi kokarin jin ta bakin ma’aikatar kula da kananan hukumomi da masarautu ta jihar, to amma haka ta bata cimma ruwa ba, don ban sami babban sakataren ma’aikatar ba,an ce dani bai gari, haka nan na ta buga wayarsa amma ba’a dauka ba, kuma babu amsar sakon kar ta kwanan dana aike masa.

To sai dai mai baiwa gwamnan jihar shawara ta fuskar harkokin siyasa Abubakar Bawa, yace bai da cikakken bayani,don haka zai bincika.

Wata majiya a majalisar dokokin jihar tace akwai batun, koda yake ba’a bayyanata a hukumance ba, wanda kuma yanzu an zura ido aga matakin da hukumomin jahar za su dauka kan batun.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG