Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Ma Goyon Bayan Radiyo Biafra- Rochas


Gwmanan Jahar Imo Rochas Okorocha, a lokacin ya neman takarar shugabancin Najeriya.

Gwamnan jahar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, Rochas Okorocha, ya nisanta al'umar Igbo da gidan Radiyo Biafra da ake zargi da watsa labaran karya da tunzura mutane.

Gwamnan Jahar Imo a Najeriya, Rochas Okorocha, ya ce al’umar Igbo da ke gabashin kasar ba sa goyon bayan manufofin da gidan Radiyo Biafra ke yadawa.

A cewar Rochas, gidan radiyon ba shi da tushe kuma manufofinsa ba daidai su ke da na al’umar Igbo ba domin sun sabawa dokar Najeriya.

“Babu wani mutum daga al’umar Igbo da ke bayansu, ba mu sansu ba kuma ba za a ce akwai wani mutumin Igbo da ya ke bayansu ba.” In ji Okorocha.

Ya kuma kara da cewa suna kallon gidan radiyon ne a matsayi matsaloli irinsu na masu yin garkuwa da mutane da na Boko Haram da Najeriya ke fama da su.

Rochas wanda ya ke cikin tawagar shugaban Najeriya da ya kawo ziyarar kwanaki hudu a Amurka ya nuna farin cikinsa ganin yadda gwamnatin tarayya ta yi maza maza ta rufe gidan radiyon.

“Muna godiya kan yadda gwamnatin tarayya ta shiga maganar da sauri-sauri aka tsaida su, mun kuma gayawa mutane da su yi watsi da su.” in ji Rochas.

Ana dai zargin gidan radiyon na Biafra da yada kalaman batanci da kuma tunzura al'umar Igbo da su yiwa Najeriya bore domin su bangare daga kasar.

A makwannin da suka gabata, hukumar da ke kula da gidajen radiyo da talbijin ta NBC a Najeriya ta ce ta rufe gidan radiyon amma akwai rahotanni da ke cewa ana jin ta a shafukan intanet.

Sai dai a wata hira da ya yi da Muryar Amurka a farkon makwan nan, Malam Ibrahim Salihu, ya ce suna shirin rufe tashar ma a shafukan na intanet.

Ga cikakkaiyar hirar da wakilin Muryar Amurka Mahmud Lalo ya yi da Rochas Okorocha:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG