Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Mu Da Halin Biyan Karin Kudin Fansa Na Miliyan 100 Da ‘Yan Bindiga Suka Nema - Iyayen Daliban Greenfield


Wasu masu garkuwa da mutane
Wasu masu garkuwa da mutane

Iyayen sauran daliban jami’ar Greenfield 20 na jihar Kaduna da suka rage a hannun ‘yan bindiga na rokon gwamnatin tarayya da ta jihar Kaduna da sauran masu ruwa da tsaki da su taimaka masu cikin gaggawa don ceto ’ya’yansu.

Shugaban iyayen yaran da ke cikin halin ha’ula’i sakamakon sace ‘ya’yansu da ‘yan bindigan suka yi, Marcus Zarmai, ya jadada bukatarsu ta neman shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da ofishinsa wajen kubutar da ‘ya’yansu kafin ‘yan bindigan su dauki muggan matakai kan daliban da sauran mutanen dake tsare a hannunsu.

A ranar 20 ga watan Afrilu, kimanin makwanni 3 da suka gabata ne ‘yan bindiga suka afkawa jami’ar Greenfield dake karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna inda suka sace dalibai da dama.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Marcus Zarmai yana cewa, masu garkuwa da mutanen na neman karin kudin fansa na naira miliyan 100 baya ga biyan naira miliyan 60 da iyaye suka tattara suka biya don a saki ‘ya’yan su ba tare da samun nasara ba.

Iyayen daliban, ‘yar wata mata dake tsare na cikin halin kakani-kayi, dimauta, matsanancin damuwa kamar yadda suka nuna a yayin zantawa da mamena labarai.

Sun yi taron manema labaran ne, don nuna damuwar kan ci gaba da tsare ‘ya’yansu da ‘yan bindigan suka yi na tsawon makwanni 3 ya sanya su a ciki a jihar Kaduna.

Haka kuma, Marcus Zarmai ya ce iyaye sun gama sayar da duk kaddara da suka mallaka sun yi amfani da su wajen biyan kudin fansa kuma ba su da halin da za su biya karin naira miliyan 100 da ‘yan bindigan ke nema daga garesu.

Hakan ya sa suka nemi gwamnatin tarayya ta kai masu dauki kamar yadda ta yi da aka sace yaran makarantar Kankara, Kagara, Jangebe da dai sauransu.

A baya-bayan nan sace dalibai domin neman kudin fansa ya zamo ruwan dare a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Najeriya, inda gwamnatin jihar ke jaddada cewa, ba za ta yi zaman tattaunawa da miyagun ba balle ta biya su kudin fansa.

Bayan ‘yan kwanaki da sace daliban, ‘yan bindigan sun kashe 5 daga cikinsu tare da yin barazanar kashe sauran idan iyayensu da gwamnati suka gaza biyan su kudin fansa na naira miliyan 800.

‘Yan bindigan sun saki daya daga cikin daliban a makonni biyu da suka gabata biyo bayan rahotannin biyan kudin fansa da ba a san nawa ba da iyayensa suka biya don a sake shi.

XS
SM
MD
LG