Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk Da Sulhun Da Ake Kokarin Yi, Duk Wanda Ya Takale Mu Za Mu Mayar Da Martani – Gwamnatin Ganduje


Gwamna Ganduje (Facebook/Muhammad Garba)
Gwamna Ganduje (Facebook/Muhammad Garba)

Wannan sabon babin sa-in-sa da aka bude tsakanin bangarorin biyu, na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan da Ganduje ya je ya yi wa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwar dan uwansa.

Gwamnatin jihar Kanon Najerya ta mayar da martani ga tsohon gwamna Dr. Rabiu Musa Kwankwaso bisa kalaman da ya yi cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ba ta ci zaben 2019 ba.

Yayin wata hira da ya yi da jaridar Punch a karshen makon da ya gabata, Kwankwaso ya yi ikirarin cewa Ganduje bai ci ba yana mai cewa wasu masu fada a ji ne daga sama “suka dora shi akan al’umar jihar.”

“Al’umar kasar nan na sane sarai cewa Ganduje bai ci zaben 2019 a Kano ba, amma wasu masu fada a ji ne suka dora shi akan al’umar da suka fi rinjaye.” Kwankwaso ya ce.

Sai dai ga dukkan alamu kalaman tsohon gwamnan na Kano bai yi wa gwamnati mai ci dadi ba, lamarin da ya sa ta yi wuf ta mayar da martani.

“Gwamnatin Kano ta yi watsi da kalaman tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya yi cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai ci zaben 2019 ba.” Wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Comrade Muhmmamad Garba ta ce.

A cewar Garba, abin takaici ne a ce tsohon gwamnan, wanda ya san yadda al’amuran zabe ke tafiya, a ce har yanzu yana kalubalantar sakamakon zaben da hukuma ta gudanar kotu kuma ta tabbatar da shi.

Sanarwar ta kuma zargi Kwankwaso da jagorantar wasu hanyoyin yin magudin zabe a 2019 musamman a kananan hukumomin da ke cikin birni inda aka saka matasa suka cika akwatunan zabe da kuri’u

“Amma hukumar zabe ta gano cewa ba a yi amfani da na’urar tantance katunan zabe ko kuma sunayen da ke cikin taskar bayanan masu zabe ba, hakan ya sa hukumar ta soke zabe ta ce bai kammalu ba.” Comrade Garba ya ce.

Yayin hirar da ya yi da Punch, Kwankwaso ya ce tun farko ma bai kamata a bar Ganduje ya tsaya takara ba.

“Akwai dalilai da za su iya sa hana shi yin takara a 2019, amma wasu manya suka tsaya tsayin daka akan sai ya ci gaba. Sai talakawa suka yanke shawara bijirewa manyan. Amma duk da haka sai suka yi amfani da karfinsu, mu kuma ba ma son abin da zai ta da husuma a Kano.”

Wannan sabon babin sa-in-sa da aka bude tsakanin bangarorin biyu, na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan da Ganduje ya je ya yi wa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwar dan uwansa, lamarin da ya bude kofar tattaunawar sulhu tsakanin manyan ‘yan siyasar biyu.

Sai dai cikin sanarwar da kwamishinan yada laraban jihar ya fitar a ranar Lahadi, ya ce ba za su nade hannu suna kallo wani ya rika takalarsu ba duk da cewa ana yunkurin yin sulhu.

“Duk da yunkurin sulhu da shugabannin jam’iyya ke yi a tsakaninsu, gwamnatin Ganduje za ta mayar da martani ga duk wanda ya yi kokarin muzanta ayyukan ci gaban da ta samar.” Kwamishinan yada labarai Comrade Garba ya ce.

XS
SM
MD
LG