Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Wanda Ya Kama Mu - Ma’aikacin Gidan Talabijan Na Channels


Ma'aikatan Channels
Ma'aikatan Channels

Ma’aikacin gidan talabijan na Channels, Kayode Okikiolu, ya musanta labarin cewa hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta kama shi da abokin aikinsa Chamberlain Usoh a ranar Alhamis.

Kayode Okikiolu ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, hukumar kula da kafafen yada labarai ta NBC ce ta gayyace su domin su ba da bayani kan wata hira da suka yi a gidan talabijan na channels, amma ba hukumar DSS ba.

Okikiolu ya kara da cewa rashin iya daukar kira a lokacin da su ke kan hanya zuwa ofishin na NBC ne ya yi sanadiyar rade-raden da aka yi ta yadawa cewa DSS ta kama tare da tsare su, inda ya mika godiya ga wadanda suka damu da lamarin da su ke ciki.

Rahotanni sun yi nuni da cewa gayyatar ma'aikatan na Channels biyu, Chamberlain Usoh da Kayode Okikiolu na tsawon wasu sa’o’i ba ya rasa nasaba da wata hira da suka yi da gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai da aka nuna a gidan talabijan din a ranar talata.

Tuni kuma da hukumar ta NBC ta aikawa gidan talabijin na channels takardar gargadi a ranar 24 ga watan Agustan da mu ke ciki, inda ta yi nuni da cewa an sabawa dokar yada labarai ta kasar, ta hanyan bari bako ya yi kalaman da ke iya haddasa rudani da rarrabuwar kai a Najeriya.

Wasikar da Hukumar NBC ta mikawa gidan talabijan na Channels kan sabawa ka'idar dokar yada labarai na kasar.
Wasikar da Hukumar NBC ta mikawa gidan talabijan na Channels kan sabawa ka'idar dokar yada labarai na kasar.
Wasikar da Hukumar NBC ta mikawa gidan talabijan na Channels kan sabawa ka'idar dokar yada labarai na kasar.
Wasikar da Hukumar NBC ta mikawa gidan talabijan na Channels kan sabawa ka'idar dokar yada labarai na kasar.

Wasu majiyoyi sun yi nuni da cewa hukumar DSS dai ta dauki sa’o’i tana yi mu su tambayoyi bayan da ta sami korafi daga NBC.

Haka kuma, wani jami’in hukumar ta DSS da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyyana cewa an gayyaci ma’aikatan gidan talabijan na Channels ne biyo bayan shigar da korafi da hukumar NBC ta yi a kan su, bisa sabawa ka’idar dokar yada labarai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Baya ga bayani kan hirar da Ortom, bayanai sun kuma yi nuni da cewa hukumar DSS ta nemi bayani daga bakin ma’aikatan biyu game da zantawar da suka yi da wani tsohon kwamandan sojin ruwa, Kunle Olawunmi, wanda ya yi zargin cewa akwai masu daukar nauyin ayyukan mayakan Boko Haram a cikin mukarraban shugaba Buhari.

Wani jami’in DSS da bai ambaci sunansa ba a bisa dalili na tsaro ya kara da cewa an yiwa ma’aikatan na Channels din masu gabatar da shirye-shiryen da suka sami rakiyar lauyoyinsu tambayoyi kan dalilin da ya sa ba su gargadi bakinsu a cikin shirin kan kalamai masu tsauri da ka iya tada hankali da raba kan kasa da suka yi ba.

Rahotanni sun kuma ce kafin a saki Okikiolu da Chambalain a daren jiya, an nemi su yi alkawarin cewa ba za su yarda irin wannan yanayin ya sake maimaita kansa ba, sai dai ma’aiktan biyu sun ce ba za su iya yin wani alkawari ba, suna masu cewa su ma’aikata ne kawai a gidan talabijin na Channels saboda haka ba’a ba su ikon yin wani alkawari a madadin kamfanin ba.

Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, shi ma ya musanta batun kama ma’aikatan gidan talabijan na Channels, kuma bai fayyace ko da gaske ne‘ batun hukumar ta gayyace su don amsa tambayoyi ba.

Idan ana iya tunawa, a ranar talata a yayin shirin safe na 'Sunrise Daily' na gidan talabijan na Channels, gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai wanda ya kasance bako a shirin, ya bayyana cewa da alamu wasu abubuwa da ake cewa game da shugaban kasa yana da boyayyiyar manufa kan Najeriya gaskiya ne, saboda a bayyane yake nuna kamar yana da ra’ayin mayar da kasar ta Fulani.

XS
SM
MD
LG