Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Wanda Ya Taba Lafiyata, inji Firayim Ministan Serbia


Firayim Ministan Serbia Aleksandar Vucic

Gano wasu makamai kusa da gidan Firayim Ministan kasar Serbia Aleksander Vochic, ya sa wasu na ganin watakila ana yunkurin kasheshi ne

A jiya Lahadi Firayim Ministan Serbia Aleksander Vucic ya baiwa jama'ar kasar tabbacin cewa yana nan lafiya kalau, kwana daya bayan da aka gano wasu makamai da aka boye kusa da gidansa, abinda yasa ‘yan sanda suka fisshe shi daga gidansa tare da iyalansa.

Da yake magana a birnin Belgrade, Vucic ya yi kashedi ga jama’a akan su guje wa danganta gano wadannan makaman da aka yi da yunkurin yi masa kissan gilla,yana cewa, “Ba wanda ya taba lafiyata.”

Makaman da ko aka gano a kusa da gidan nasa sun hada da gurneti da ake sarrafawa da hannu,da roka,da bindigogi, sai kuma harsasai.

Wadannan sune aka samu a cikin wani kwararo a cikin daji kusa da gidansa, inda sau tari nan tawagar motocinsa ke bi idan zasu gida kuma motocin galibi sukan rage gudu ne idan sun kawo wurin .

Ita dai kasar Serbia tana fama da yawan tarin makamai da aka bari tun lokacin yakin da aka yi na Balkan a shekarar 1990. Ba sabon abu ba ne mutane suyi watsi da wadannan makamai domin gudun kar ‘yan sanda su same su dasu.

XS
SM
MD
LG