Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za A Bude Iyaka Da Amurka Ba Sai Bayan Wata Guda-Canada


Justin Trudeau na Canada da Donald Trump

Kasar Canada ta sanar a jiya Juma’a cewa zata ci gaba da kulle iyakarta da Amurka ga matafiya da basu da muhimmin abin yi zuwa wata na gaba, yayin da Amurka ke ci gaba da zama kasar da tafi yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a duniya da ma yawan wadanda suka mutu da cutar.

“Yan Canada da dama suna bayyana damuwar su a kan rashin bude iyakar, bayan Canada ta yi nasara dakile yaduwar annobar.

Mutum dubu 123 ne suka kamu da coronavirus a Canada kana sama da wasu dubu tara suka mutu da cutar a cewar jami’ar John Hopkins. Sabanin haka, Amurka tana da sama da mutum miliyan biyar da dubu dari biyar da suka kamu da cutar, wato kashi daya cikin hudu na adadin kamuwa da cutar a duniya, kana wasu dubu 167 sun mutu a cewar jami’ar Hopkins.

A kasar Spain, ministan kiwon lafiya ya sanar da karin matakan takaita harkoki a jiya Juma’a domin dakile karuwar coronavirus. Minista Salvador Illa yace za a rufe duk gidajen rawa a fadin kasar. Ya kuma ce za a haramta shan tabar sigari a cikin jama’a, idan masu shan sigarin basu bada nisar akalla mitoci biyu tsakanin su ba.

A halin da ake ciki, matsalar da tsarin bada rahoton kamuwa da COVID-19 a jihar California ya samu yasa ya bai lissafa kusan mutum dubu dari uku da suka kamu da cutar a cewar jami’an jihar.

Bayanai daga jaridar New York Times a jiya Juma’a sun nuna California ce jihar Amurka da ta fara samun mutum dubu dari shida da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 da wasu dubu 11 da suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG