Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Za Mu Yi Katsalandan a Zaben Sabon Sarkin Kagara Ba - Gwamnatin Neja


Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello (Hoto: Twitter, Gwamnatin jihar Neja)

Al’ummar masarautar Kagara a jihar Nejan Najeriya na ci gaba da zaman jiran sabon sarkinsu bayan rasuwar tsohon sarkin Mai Martaba Alh. Salihu Tanko a cikin makon da ya gabata

Masarautar Kagaran dai tana da mutum14 a matsayin masu zaben sabon sarki.

Sannan tana da Gidan Sarauta 6 da suka hada da Gunna,Tagina, Kusharki, Kongoma, Uragi, da Kuma Katunga, kamar yadda Tambarin Kagara Hon. Danladi Umar Abdulhameed ya ce.

“Sarautar ba wai ana bayayya ba ne (karba-karba) wanda ya cacanta a wadannan gidajen, wanda Allah ya ba, shi za a ba.” In ji Abdulhameed.

Gwamnatin Jihar Nejan dai ta ce ba za ta yi katsalandan ba a cikin nadin sabon Sarkin Kagaran in ji Sakataren Gwamnatin Jihar Alh. Ahmed Ibrahim Matane.

“Gwamnati ba ta so ta yi sauri, sai an tabbata cewa an dubi wannan doka da ta kafa wannan masarauta, su waye masu zaben sarki. Gwamnan jihar Neja ya ba kwamishinan kananan hukumomi da kwamishinan shari’a da kuma sakatarensa na cikin gida (umurni), don su tabbatar da cewa dokar da aka sa hannu da ita za a yi amfani da ita.” Matane ya ce.

Marigayi Sarkin Kagara, Mai Martaba Alhaji Salihu Tanko
Marigayi Sarkin Kagara, Mai Martaba Alhaji Salihu Tanko

Da aka tambayi sakataren gwamnatin ko yaushe za a samu damar nada sabon sarki, sai ya ce, “ka san mu a gwamnatance, muna jiran su (masu zaben sarki a gargajiyance), muna kuma fatan za su yi abin da ya kamata, ko da yake an dade ba a yi ba.”

A yanzu dai Al’ummar Masarautar Kagaran na matukar bukatar samun jajirtaccen sabon Sarki bisa La’akari da yadda yankin ke fuskantar kalubale irin na Tsaro,

Da yammacin ranar Talata gwamnatin jihar Nejan ta sanar da rasuwar Sarkin Kagara mai daraja ta daya mai martaba Alhaji Salihu Tanko.

Margayi ya rasu yana da shekaru 102 kuma ya hau kan karagar mulki ne a shekarar 1981, kenan ya share kimanin shekaru 35 akan karagar mulki, ya rasu yabar mata 2 da yara 15 da kuma jikoki da dama, tuni dai aka yi jana’izarsa a fadar sarkin da ke garin Kagarar.

XS
SM
MD
LG