Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Zan Yarda A Samu “Cabal” A Gwamnatinmu Ba – Atiku


Hira Ta Musanman Da Atiku Abubakar A Washington
please wait

No media source currently available

0:00 0:24:05 0:00

Hira Ta Musanman Da Atiku Abubakar A Washington

Jama’a da dama a Najeriya, ciki har da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, su n yi ikirarin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sakar wa wasu mutane ragamar tafiyar da al’amuran kasar, ko da yake, Buharin ya musanta hakan a wata hira ta daban da ya yi da VOA a 2019.

Dan takararar mukamin shugaban kasa karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce idan ya lashe zaben 2023, ba zai bari a samu abin da ake kira “Cabal” a gwamnatinsa ba.

‘Cabal,’ kalma ce ta harshen Ingilishi da ake amfani da ita a fagen siyasar Najeriya, wacce ke nufin wani rukunin ‘yan siyasa da ke jan ragamar gwamnati mamakon shugaban kasa.

“Ba wani Cabal da za a samu, Waziri ne (Atiku) zai ja ragamar komai.” Atiku ya ce a wata hira da ya yi ta musamman da shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka Aliyu Mustapha Sokoto, yayin ziyarar da yake yi a Washington.

Jama’a da dama a Najeriya, ciki har da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, na ikirarin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sakar wa wasu mutane ragamar tafiyar da al’amuran kasar, ko da yake, Buharin ya musanta hakan a wata hira ta daban da ya yi da VOA a 2019.

“Su fadi abin da ‘Cabal’ din suka shirya suka tilasta ni na yi, su fadi abu daya.” Buhari ya kalubalanci masu ikirarin a wancan lokacin.

Atiku na ziyara ne a Amurka inda yake tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar kan batutuwa da suka shafi tsaro, tattalin arziki da zaben da za a yi a Najeriya a badi.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Matsalar Tsaro

Dangane da batun matsalar tsaro a Najeriya, Atiku ya ce, yi wa kundin tsarin mulki Najeriya ne mafita ga kasar.

“Ta yadda za mu bullo shi ne, a gyara tsarin mulki, domin idan muna so mu ba jihohi da kananan hukumomi irin wadannan aiki, tilas ne mu gyara tsarin mulkin Najeriya, amma kafin haka, muna da niyyar mu kara daukan ma’aikata, musamman wajen harkokin ‘yan sandan da kuma masu tsaron lafiya, kuma mu samar masu kayan aikin yi.” Atiku ya ce.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce za kuma su nemi hadin kan alkalai wajen ganin an yanke wa wadanda aka samu da laifi hukunci ba tare da bata lokaci ba, yana mai nuna goyon bayansa ga hukuncin kisa ga rukunin mutanen da suka aikata laifukan da suka shafi ta’addanci.

Atiku wanda ya rike mukamin na mataimakin shugaban kasa a zamanin mulkin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, ya kaucewa yin magana kan tsohon maigidan nasa da aka tambaye shi yadda dangantaka take a tsakaninsu a yanzu.

"Kai dai a je kawai." Atiku ya fadawa Aliyu Mustapha.

Atiku ya kuma lissafa rashin jituwar da suka samu da Obasanjo a wancan zamanin, a matsayin daya daga cikin dalilan da suka sa bai samu nasara a zaben 2011.

Sauya Fasalin Kudin Najeriya

Game da batun shirin da babban bankin Najeriya na CBN ke kokarin aiwatarwa kan sauya fasalin wasu kudaden Najeriya, Atiku ya ce ba shi da masaniya kan dalilan da suka sa gwamnatin take so ta aiwatar da wannan shiri.

Wata kididdiga da babban bankin Najeriya na CBN ya yi, ta nuna cewa sama da kashi 80 na daukacin kudin kasar na hannun jama’a, batun da Atiku ya danganta da rashin isassun bankuna a sassan kasar.

Matatun Man Fetur Din Najeriya

Wani fanni da ya jima yana ci wa Najeriya tuwo a kwarya shi ne na matatun man fetur din kasar da suka kasance ba sa aiki yadda ya kamata, inda Atiku ya ce bai sauya matsayarsa ba kan yadda zai tafiyar da matatun idan har suka kafa gwamnati.

“Matsayar da na dauka kan wannan batu ba sabon abu ba ne, na riga na fada tun shekarun baya da suka wuce, sayar da su zan yi. Domin idan ka ba ‘yan kasuwa, za su fi tafiyar da wannan kamfanonin.”

Atiku ya kara da cewa, ‘yan kasuwa suna da karfin da za su iya tafiyar da matatun man ta hanyar gyara su yadda ya kamata.

Aliyu Mustapha Sokoto, yana hira da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar
Aliyu Mustapha Sokoto, yana hira da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar

Dangane da batun matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya, Atiku ya ce za su tabbatar da cewa duk wanda aka kai shi kara kotu an yanke masa hukuncin cikin lokaci.

“Wannan zai nuna wa mutane cewa gwamnati da gaske take yi," In ji Atiku

Rikicin Cikin Gida Na PDP

Game da batun rikicin gida da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku ya ce har yanzu ba a samu cikakken sulhu ba.

“Ba a samu cikakken shiri ba, amma mun yi gaba, na gaba ya yi gaba, na baya sai labari, ba ni da wata damuwa.” Atiku ya ce.

Ya kara da cewa shi ba ya goyon bayan a sauya shugaban jam’iyyarsu ta PDP domin a cewar shi, an doshi zabe.

“Bai dace a wannan lokaci ka ce za ka yi canjin shugaban jam’iyya ba, alhali ga mu nan dab da zabe." Atiku ya ce.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar lokacin wata hira da VOA ta yi da shi a 2019
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar lokacin wata hira da VOA ta yi da shi a 2019

Atiku har ila yau ya ce suna da kwarin gwiwa hukumar zabe ta INEC za ta kamanta gaskiya a zaben wanda za a yi a watan Fabrairun badi.

“Domin ka ga sun yi zabe guda biyu wadanda muka yaba musu, sun yi na Ekiti mun yaba musu, sun yi na Osun mun yaba musu, kuma shugaban kasa ya tabbatar mana cewa lallai, zai tabbata an yi zabe cikin adalci da kuma gaskiya.” In ji Atiku.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma ce zuwansa Amurka, ba yana nufin gwamnatin Amurkar za ta goya masa baya ba ne a zaben na 2023.

Ga somin tabin da muka tsakuro daga a hirar:

Ba Zan Yarda A Samu “Cabal” A Gwamnatinmu Ba – Atiku- 3'56"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00

XS
SM
MD
LG