Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba’amurke Dan asalin Najeriya Mai Kamfanin Jiragen Sama


 Matukin jirgin sama ba'amurke dan asalin Najeriya Anthony Oshinuga
Matukin jirgin sama ba'amurke dan asalin Najeriya Anthony Oshinuga

Anthony Oshinuga, da ne ga wasu ‘yan Najeriya da suka yi kaura zuwa Amurka, yanzu haka kuma ya mallaki wani dan karamin kamfanin jiragen sama da ke daukan masu yawon bude ido a California.

Ya fara sha’awar mu’amulla da jiragen sama ne tun ya na dan shekara biyar, a lokacin da su kai ziyara filin tashin jirage da iyayensa.

“A lokacin na gayawa mahaifina, wannan harkar na ke so na yi idan na girma.” Oshinuga ya ce.

Asalin iyayensa sun fito ne daga jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, amma kuma shi an haife shi ne a birnin Austin da ke jihar Texas.

“An haife ni ne a Austin da ke Texas, ni ne mutum na farko a cikin danginmu da aka haifa a nan Amurka, duk ‘yan uwana na can gida a Najeriya.”

Dan karamin kamfanin na sa ya na safara ne tsakanin Temecula a California, a arewacin San Diego inda ake samun da kayan sha.

“Mu kan hada kai da manyan kamfanoni biyu da su ke samar da kayan sha na wine a yankin. Mu kan kwashe minti 30 muna daukan masu yawon bude ido muna zagayawa da su a saman Temecula, inda sukan je su sha kayan abinci na ruwa.”

Oshinuga ya taba shiga wata gasar tuka jirage a shekarar 2014 inda ya zo na hudu cikin mutane 25.

XS
SM
MD
LG