Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Bankin Najeriya Ya Kama Hanyar Karya Darajar Nera


Nera, takardar kudin Najeriya

Babban Bankin Najeriya ya dauki wani mataki na wucin gadi akan Nera, wato kudin kasar lamarin da masana ke ganin zai kaiga karya darajar kudin nan gaba.

Masana tattalin arziki a kasar kamar yadda suka hango suna ganin matakin Babban Bankin na wucin gadi zai kaiga karya darajar Nera daga karshe.

Alhaji Sha'aibu Idris wani masanin tattalin arziki dake birnin Legas ya yi fashin baki akan makasudin taron da babban bankin kasar ta gudanar da ma'anar taron..Yace taron da suka gama kusan abu daya ne ainihin makasudin taron.. Yace kawuna sun rabu akan farashin da za'a sayi dalar Amurka.

Akwai wadanda suke ganin babu hujjar rage darajar Nera saboda kasashen duniya da yawa da suka karya darajar kudadensu basu samu biyan bukata ba. Misali ita ce kasar Rasha da ta karya darajar kudinta da kashi 40 kuma har yanzu tana cikin tabo. Kasar Masar ma tayi hakan amma bata samu biyan bukata ba.

Maimakon a karya darajar Nera masu kamfanoni su dinga shigo da kayan da zasu sarafa cikin gida. Irinsu idan kayan da zasu sarafa na dole ne domin a tallafawa talakawa sai a sayar masu da dala da rahusa.

Saidai wadanda suke son a karya darajar Nera sun fi yawa kuma sun fi baki domin su ne suke da kafofin yada labarai dalili ke nan suka fi kowa magana.

Alhaji Idris yace ko an karya darajar Nera dala ba zata samu ba sai kasar ta sayar da man fetur wanda kuma farashinsa ya fadi daga dala 120 zuwa dala 50. Da kasar tana fitar da gangar mai miliyan 2.2 kullum amma yanzu da kyar take fitar da miliyan 1.4.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG