Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Sifeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Sake Watsi Da Goron Gayyatar 'Yan Majalisa


 Ibrahim Idris, babban sifeton 'yan sandan Najeriya
Ibrahim Idris, babban sifeton 'yan sandan Najeriya

A karo na biyu, babban sifeton ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya ki amsa gayyatar da majalisar dattawan Najeriya ta yi masa.

A karo na biyu babban sifeton ‘yan sandan Najeriya Alhaji Ibrahim Idris ya ki ya bayyana a gaban majalisar dattawan Najeriya.

Majalisar ta bukaci ya bayyana a gabanta ya amsa zargin da aka yi na cewa wasu jami’an ‘yan sanda sun ci zarafin Sanata Dino Melaye wanda ya shiga hannunsu makon da ya gabata.

Batu na biyu da majalisar take son babban sifeton ya yi mata bayani shi ne akan kashe kashen da ake yi a wasu jihohin kasar.

Shugban majalisar Dr. Bukola Saraki a jawabin da ya yi ya ce irin matakan da ‘yan sandan ke dauka na yiwa dimokradiyar kasar barazana. A cewarsa ba majalisar kadai babban sifeton ya rena ba hatta ma shugaban kasa saboda lokacin da ya bashi umurnin ya tafi jihar Binuwai bai je ba.

Dr. Saraki ya bukaci shugaban masu rinjaye a majalisar da ya jagorancesu zuwa gaban shugaban kasa su bayyana masa irin halin da suka tsinci kansu a ciki dangane da babban sifeton ‘yan sandan.

Shugaban kwamitin dake kula da harkokin ‘yan sanda Sanata Abu Ibrahim ya yi karin haske akan tuntubar da zasu yi da Shugaba Buhari. Ya ce shi da Sanata Ahmed Lawal shugaban masu rinjaye zasu sami shugaban kasa su yi masa magana kan babban sifeton ‘yan sandan da kuma neman yadda za’a sa ya bayyana gaban majalisar.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG