Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ADAMAWA: Jiya Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane Da A Mubi


Harin kunar bakin wake a Mubi da ya auku a wani masallaci

Jiya harin da wasu 'yan kunar bakin wake suka kai garin Mubi dake jihar Adamawa ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikata wasu da yanzu suke samun jiya a asibitin gwamnatin tarayyar Najeriya dake Yola babban birnin jihar

Mutane da dama ne suka mutu a jiya talata lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a wajen masallaci dake garin Mubi a jihar Adamawan Najeriya.

Sai dai kawo yanzu bawani ko wasu da suka dauka alhakin aikata wannan aika-aikan, sai dai wannan harin yana da alamun irin hare haren da kungiyarBoko haram ke kaiwa.

Baya ga mutane masu tarin yawa da suka mutu haka kuma rahotanni sun bayyana cewa da damasun samu rauni.

Shedun gani da ido sunce dan kunar bnakin waken ya tada bomb din ne a harabar masallacin, kuma ana cikin juyayin tashin bomb na farko bayan dan kankanin lokaci kuma sai na bomb na biyu ya sake tashi, a tsakanin mutane masu sallah da suka ranta na kare daga tashin bam na farko zuwa wata kasuwa dake kusa da masallacin da bomb din ya tashi.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG