Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Dakatar Da Ayyukan SARS, STS, IRT


Shugaban Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu
Shugaban Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu

Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ya dakatar da kan rundunar nan ta musamman mai yaki da ayyukan ‘yan fashi da makami, Federal SARS,

Sauran rundunonin da ya dakatar sun hada da Rundunar Dabaru na Musamman (STS), Rundunar Kai Agaji ta Leken Asiri (IRT).

A cikin wata sanarwar da rundunar ’yan sanda ta fitar, IGP Adamu ya bayar da umarnin haramta musu cigaba da gudanar da ayyukan sintiri da kafa shigayen binciken ababen hawa da sauran ayyukan tsaro akan manyan hanyoyi.

Sanarwar da kakakin rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, DCP Frank Mba, ya sanyawa hannu ta ce an kuma haramtawa ‘yan sandan fita aiki ba tare da sanya kayan sarki ba.

Daukar wannan mataki dai ya biyo bayan yadda rundunar ta bankado irin aika aika da jami’anta ke tafkawa suna fakewa da guzuma suna harbin karsana, wanda hakan ya sabawa ka’idoji da dokokin aikin Dan Sanda.

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan ya fito karara ya nuna bacin ransa bisa yadda ‘Yan Sandan suke keta hurumin sirrin ‘yan kasa ta hanyar binciken wayoyinsu da komputocinsu inda ya ja musu birki da cewa ya isa haka. Yace,

“Ya kamata su mai da hankalinsu wajen bayar da bayanai akan batutuwan fashi da makami, satar mutane da sauran muggan laifuka lokacin da bukatar hakan ta taso."

IGP Adamu, ya bayyana cewa rundunar ta (FSARS) da sauran ‘yan sanda suna da muhimmanci matuka a rundunar wajen tunkarar manyan laifuka a Kasar.

Ya kuma yi Allah wadai da duk wani aiki na rashin kwarewa, cin zarafin bil ‘adama da kuma nuna son rai da wasu ma’aikatan hukumar ke yi.

Wani Masanin Tsaro, Yahuza Ahmed Getso yace akwai matakan da ya kamata a dauka domin kawo gyara a wannan rukunai na ‘Yan Sanda.

Yace abu na farko shi ne a tabbata an canja tsarin daukan jami’an ‘Yan Sandan, a kuma dinga tura su wajen aiki ba tare da nuna suna da wasu iyayen gida ba da wadan da ke shafaffu da mai da wadanda basu da kowa ba.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:

BABBAN SUFETON 'YAN SANDAN NIGERIA YA DAKATAR DA FSARS
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00


Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG