Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Taron Jam’iyyar APC a Abuja


APC

Jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da babban taronta a Dandalin Eagle dake babban birnin Abuja.

Karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ake gudanar da babban taron na APC, inda wakilai 6,800 zasu kada kuri’a a zaben sabbin shugabannin jam’iyyar, cikin tarin ‘yan takara da suka kai yawan 179.

Shugaban kwamitin tantancewa Sanata Ahmed Sani, ya ce Adams Oshiomhole, ya tsaya takara ba hamayya, kuma wasu kujerunma ta hanyar sasantawa za a fitar da gwanaye.

A cewar sakataren jam’iyyar APC Mai Mala Buni, duk wannan tsari dai salo ne na tsarin APC da yace zai samar da masalaha.

Wasu ‘yan jam’iyyar da suka halarci babban taron sun nemi a tabbatar da adalci, ganin yadda aka kafa jam’iyyar kan adalci, wanda hakan yasa aka zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG