Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Kotun Kenya Ta Ci Tarar Wasu Manyan Jami'an Gwamnati Saboda Kin Bin Umurninta


Alkalin babbar kotun Kenya George Odunga
Alkalin babbar kotun Kenya George Odunga

Biyo bayan bijirewa umurnin babbar kotun Kenya da ministan harkokin wajen kasar da babban sifeton 'yan sanda dadaraktan shige da fice na kasar suka, kotun ta ci tararsudalar Amurka dubu biyu biyu kowanensu

Wata Babbar kotu a Kenya taci manyan jami’an gwamanti kasar su uku tarar dala dubu biyu kowanensu bisa laifin bijirewa umarnin kotun, da suka hada da sakin wani madugun yan adawa Miguna Miguna. Hukuncin ya nuna jani-in-jaka na tsawon wata tsakanin bangaren zartaswa dana shari’ar game da rashin fahimtar da aka samu a zaben shugaban kasa a bara.

Ministan harkokin cikin gida na Kenya Fred Matiangi da sufeto Janar na yan sanda Joseph Boinnet da kuma shugaban hukumar shige-da fice- Gordon Kihalangwawere basu bayyana a kotu jiya Alhamis ba.

A kan haka ne kowane daya daga cikin mutane ukun zai biya tarar kudin Kenya shilin dubu dari biyu, wanda yayi daidai da dalar Amurka dubu biyu. Za a kuma fidda adadin wannan kudi a cikin albashinsu na sabon wata.
Alkali George Odunga shine ya yanke wannan hukunci.
Mai magana da yawun hukumar harkokin cikin gida yaki yin bayani a kan wannan hukunci, yayin da Muryar Amurka ta tuntubeshi.

Al’ummar Kenya sun wayi gari da safiyar jiya Alhamis suka ji an tasa keyar Miguna a karo na biyu a cikin dare zuwa kasar Dubai. Wani lauyan kare hakkin bil Adama kuma mataimakin Miguna, shine ya fadawa shirin Muryar Amurka na "Daybreak Africa" cewa an tilastawa Miguna barin kasar bayan da aka dirka masa magani.
Lauyoyi a birnin Nairobi sun saka kyalle mai ruwan dorawa a jiya Alhamis don nuna rashin amincewar su kan wannan mataki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG