Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KENYA: Lauyan Da Aka tasa keyarshi zuwa Canada Ya Shigar Da Kara


Miguna Miguna

Lauya Miguna Miguna da hukumomin kasar Kenya suka kora bisa zargin cin amanar kasa domin halartar bukin rantsar da madugun adawa Raila Odinga yace gwamnatin bata da hujja, ya kuma jadada cewa, madugun adawan ne halaltaccen shugaban kasa.

Wani lauyan kasar kenya da aka tasa keyarshi zuwa Canada farkon makon nan bisa zargin cin amanar kasa, ya kalubalanci korarshi daga kasar a kotu, yana neman a bashi izinin komawa kasar ta Afrika yayinda yake jadada cewa, madugun adawa Raila Odinga ne halaltaccen shugaban kasar ba Shugaba Uhuru Kenyatta ba.

An tasa keyar Miguna Miguna, wanda yake da izinin zama dan kasashen biyu Kenya da kuma Canada, zuwa birnin Toronto ranar Talata bayanda ya halarci kwarya kwaryar bukin rantsar da Odinga a birnin Nairobi ranar talatin ga watan Janairu. Miguna kuma yana daya daga cikin lauyoyin Odinga.

An kama Miguna ne ranar Jumma'a da ta gabata a garinsa Runda, kana ranar Talata hukumomin kasar Kenya suka tilasa shi shiga jirgin KLM da ya tashi da dare daga Nairobi zuwa Toronto ta Amsterdam. Tasa keyarshi zuwa Canada da aka yi ya saba umarnin da babbar kotun kasar Kenya ta bayar cewa, a gabatar da shi gaban alkali a Nairobi ranar Laraba, bayan kwanaki biyar da kama shi.

Ministan harkokin cikin gida ya buga a shafin Twitter cewa, Miguna ya sadakar da zamansa dan kasar Kenya shekaru da dama da suka shige, ya zama dan kasar Canada, bayanda aka bashi mafaka a kasar lokacinda yake karatun aikin lauya a jami'ar Toronto.

Miguna haifaffen kasar Kenya ya musanta cewa ya sallama kasarsa ta asali, ya kuma bukaci a nuna takardar da ta nuna haka idan gwamnati tana da hujja.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG