Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Adalci A Raba Mukaman Gwamnatin APC-Atiku Abubakar


Alh. Atiku Abubakar
Alh. Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa karkashin tututar Jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar yace babu adalci a yadda aka raba mukamai a gwamnatin Buhari.

A cikin hirarshi da Sashen Hausa, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriyan yace sa kabilanci da addini a harkokin mulki ko raba mukamai rashin adalci ne, kuma yana daga cikin babbar matsalar da ake fuskanta a Najeriya.

Da yake bayyana yadda zai tunkari wannan matsala, Alhaji Atiku yace idan shugaba ya yi adalci ya ba kowanne addini da kuma kowanne bangare hakinshi za a zauna lafiya. Yace “idan aka dubi shugabancin jami’an tsaron Najeriya gaba daya, kusan wajen mutum ashirin, a cikin wajen mutum ashirin din nan, wata kila mutum daya ne ko biyu daga kudu, sauran duk daga arewa ne, kuma a ce kusan yawancinsu addini guda. Kaga ba a nuna adalci a nan ba.”Alhaji Atiku yace dokokin Najeriya har ma da addini ya bukaci cewa, idan Allah ya baka shugabanci ka yi adalci.

Dan takarar shugaban kasar na jam’iyar PDP ya bayyana cewa, ana fama da yawan tashin hankali ne a arewacin Najeriya domin su ne suke da filayen noma kuma dabbobi a arewa suke. Sai dai ya bayyana rashin fahimtar abinda ya kawo fitina yanzu kasancewa an zauna tare kaka da kakanni lafiya. Yace tsame sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma na gargajiya a tsarin shiga tsakanin makiyaya da manoma yana daga cikin dalilan da suka haifar da rikicin manoma da Makiyaya. Ya kuma bayyana cewa matakin farko da zai dauka na shawo kan wannan matsalar idan ya zama shugaban kasa shi ne zaunawa da bangarorin domin fahimtar juna.

A nashi bayanin, Shugaba Muhammadu Buhari da yake neman wa’adin mulki na biyu karkashin tutar Jam’iyar APC ya bayyana cewa, tashin hankalin da aka shiga a Libya yana daya daga cikin dalilan da suka sa ake samun tashin hankali a Najeriya. Abinda ya kai ga makiyaya dake yawo da sanda suka fara daukar bindiga.

Shugaba Buhari yace an sa kabilanci da addini a batun rikicin Fulani da Makiyaya, amma a zahiri, wahalar da aka samu ita ce shigowar Sahara da yawan mutane, da kuma barnar da aka yiwa tsarin da shugabanni magabata kamar su Sardauna suka yi. Inda aka yi burtali da makiyaya, aka yi dam-dam aka kuma sa famfo mai amfani da iska, wadanda masu hali suka dauka suka maida manyan gonaki, ya zama sanadin matsalar da ake ciki yanzu. Yace mutanen da ake kashewa a Zamfara sun fi wadanda ake kashewa a Taraba da Benuwe jimlarsu in an hade yawa, amma sai a rika cewa, sha’ainin addini ko kabilanci ne.

Saurari wannan bangaren hirar da Aliyu Mustapha ya yi da ‘yan takarar manyan jam’iyun siyasar Najeriya, Shugaba mai ci, Janar Muhammadu Buhari na jam’iyar APC, da kuma dan takarar babban jam’iyar hamayya PDP tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa.

Hira Da Buhari da Atiku PT2-11:43"
please wait

No media source currently available

0:00 0:11:43 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG