Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Babu Cikakken Bayani Akan Dalilin Juyin Mulkin Myammar


An bukaci sojojin da suka yi juyin Mulki, da su yi bayani mai gamsarwa, akan dalilin juyin mulkin.

Bayan wasu sa'o'i da sojojin Myanmar suka ayyana dokar ta baci a jiya Litinin, har yanzu akwai karancin bayanai game da abin da ke faruwa da kuma dalilin hakan.

Katse hanyoyin sadarwa da yawa da dokar hana fita, kana da kuma dokar data kasance wacce aka tsara don takaita yaduwar Korona, sun takaita hanyoyin kaiwa ga talakawan kasar ta Burma.

Da safiyar jiya Litinin ne, wani jawabi da aka yada ta gidan talabijin, mallakar sojoji ya ce, akwai “mummunar magudi a rajistar masu kada kuri’a lokacin babban zaben, wanda hakan ke karan-tsaye ga batun tabbatar da dorewar dimokaradiyya.”

A cewar, sanarwar zargin magudin da aka yi a zaben na watan Nuwamba, ya haifar da zanga-zanga da sauran ayyukan da ke lalata tsaron kasa, don haka jami’ai ke ayyana dokar ta-baci a duk fadin kasar na tsawon shekara guda, “Don yin aikin tantance sunayen masu jefa kuri’u da kuma daukar mataki.”

Sashen Burma na Muryar Amurka ya yi magana da wasu ‘yan Majalisar da wasu 'yan kasar, duk da kalubalen da ake fuskanta. An nemi sabuwar gwamnatin soji da ta yi karin bayani baya ga bayanan da ta yi a hukumance. Ba ta amsa ba saboda dalilan da su ka hada da katsewar hanyoyin sadarwa.

XS
SM
MD
LG