Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kama Aung San Suu Kyi Da Wasu Jami’an Gwamnatin Myanmar


Tsohon Hoto: Aung San Suu Kyi. A watan November 13, 2017.

Gidan talbijin din sojin kasar Myanmar na Myawaddy, ya bayyana cewa dakarun kasar sun karbe ikon tafiyar da mulkin kasar karkashin dokar ta-baci.

Sojojin sun dakatar da gwamnatin kasar ne bayan da hukumomi suka gaza yin komai kan zargin da sojojin suka yi cewa an tafka magudi a zaben kasar da aka yi a watan Nuwamba.

Wannan sanarwa na zuwa ne sa’o’i bayan da aka kama shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi da wasu kusoshin jam’iyya mai mulki, abin da ake ganin ya yi kama da juyin mulki.

Wannan lamari na faruwa ne yayin da ake shirin rantsar da ‘yan majalisar dokokin kasar.

Wani kakakin jam’iyya mai mulki ta NLD, ya tabbatar da kama Aung San Suu Kyi da shugaba Win Myint a ranar Litinin.

Wata sanarwa da Fadar White House ta fitar ta ce, “Amurka ta samu wani rahoto mai ta da hankali, wanda ke nuna cewa sojojin Burma sun dauki wasu matakai na kassara tsarin dimokradiyya.”

Sanarwar ta kara da cewa, muna kira ga “sojoji da dukkan jam’iyyu da su bi tsarin dimokradiyya da doka da oda a kuma saki duk wadanda aka kama a yau.”

XS
SM
MD
LG