Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Hujjar Da Ke Nuna Cewa Pakistan Ta San Inda Osama Ya Buya In Ji Gates


Marigayi Osama bin Laden

Sakataren Tsaron Amurka Robert Gates ya fadi jiya Laraba cewa babu shaidar da ta nuna cewa matakin sama na gwamnatin Pakistan na sane da inda shugaban al-Ka’ida Osama bin Laden yake, to amman duk da haka ya yi imanin cewa mai yiwuwa ne akwai wani a Pakistan da ya san inda dan ta’addan da aka fi nema a duniya ya boye.

Sakataren Tsaron Amurka Robert Gates ya fadi jiya Laraba cewa babu shaidar da ta nuna cewa matakin sama na gwamnatin Pakistan na sane da inda shugaban al-Ka’ida Osama bin Laden yake, to amman duk da haka ya yi imanin cewa mai yiwuwa ne akwai wani a Pakistan da ya san inda dan ta’addan da aka fi nema a duniya ya boye.

Da ya ke jawabi wa manema labarai a Pentagon, Gates ya ce a gaskiya ma dai shi ya ga shaidar da ta nuna cewa manyan jami’an gwamnatin Pakistan bas u sani ba. Ya lura cewa tuni ma Pakistan ta azabtu fiye da kima saboda shan kunya da kuma ganin yadda dakarun Amurka na musamman su ka yi nasarar kaddamar da samamamen sirri can cikin kasarta, suka kashe wanda ya kirkiro kungiyar al-Kaida.

Gano bin Laden da aka yi a birnin Abbottabad na Pakistan mai cike da kayan soji ya janyo ayar tambaya na ko dai wasu ne a rundunar sojin Pakistan ko hukumar leken asirin kasar su ka boye shi.

Wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka sun bukaci gwamnatin Obama ta yi nazarin sahihancin aniyar Pakistan, ta yaki da kungiyoyin ta’addanci kafin a sake bai wa kasar ta Pakistan karin tallafin inganta matakan tsaro.

Gates ya ce ya yadda ‘yan Majalisar na da hujjar nuna fushi, to amman shi bai ganin ya kamata Amurka ta daina taimakawa Pakistan. Ya kara da cewa yakamata Amurka da Pakistan su cigaba da tafiya tare don su tsira tare

A halin da ake ciki kuma kungiyar al-Ka’ida ta fitar da wani faifan maganar Osama bin Laden, da aka dauka ‘yan kwanaki kadan kafin rasuwarsa.

Wata cibiyar lura da al’amura da ke Amurka, mai suna SITE, ta fadi jiya Laraba cewa a wannan faifan maganar, tsohon shugaban na al-Kaida ya yaba da guguwar canjin da ke kadawa a fadin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka , sannan ya nuna farin cikinsa da nasarar zanga-zangar Misra da Tunisia.

A wannan faifan maganar, bin Laden ya yi jawabi ga masu zanga-zangar sannan ya basu wasu shawarwari da kuma dabaru.

XS
SM
MD
LG