Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Al-Qaida ta gabatar da jawabin marigayi Osama Bin Laden


Shugaban Al-Qaida marigayi Osama Bin Laden.
Shugaban Al-Qaida marigayi Osama Bin Laden.

Kungiyar Al Qaida ta gabatar da jawabin marigayi Osama Bin Laden da aka dauka a faifai wanda a ciki shugaban na Al Qaida yake yabawa guguwar zanga zangar nuna rashin amincewa dake kadawa a gabas ta tsakiya. Sakon na mintoci goma sha biyu da aka sa a wani dandalin yanar gizo, takamame ya ambaci yujin yuja halin da aka yi Tunisia da Masar a yayinda yayi hasashen cewa guguwar canji zata dabaibaiye illahirin kasashen Musulmi.

Kungiyar Al Qaida ta gabatar da jawabin marigayi Osama Bin Laden da aka dauka a faifai wanda a ciki shugaban na Al Qaida yake yabawa guguwar zanga zangar nuna rashin amincewa dake kadawa a gabas ta tsakiya. Sakon na mintoci goma sha biyu da aka sa a wani dandalin yanar gizo, takamame ya ambaci yujin yuja halin da aka yi Tunisia da Masar a yayinda yayi hasashen cewa guguwar canji zata dabaibaiye illahirin kasashen Musulmi. Bin Laden bai ambaci kasashen Libya da Syria da Bahrain ko Yamal ba, wuraren da masu hankoron ganin an kafa mulkin democradiya basu samu nasarar hambarar da gwamnitocinsu ba. A sakon da aka gabatar jiya laraba, marigayi Osama Bin Laden yayi kira ga masu zanga zangar da suyi amfani da wannan dama da suka samu, su hambarar da azalumen gwamnitoci. Ya zargi shugabanin Larabawa da laifin maida kansu gumaka kuma suna amfani da kafofin yada labaru domin su ci gaba da kasancewa akan mulki. Haka kuma kungiyar ta Al Qaida ta bada shawara ga yujin yujin halin dake bazuwa tana kira ga matasan Musulmi da su nemi shawarwari daga wadanda suka grime su domin cimma burorinsu. A ranar biyu ga wannan wata na mayu sojojin Amirka suka kashe Osama Bin Laden a sumamen da suka kai kasar Pakistan.

XS
SM
MD
LG