Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Kwakkwarar Shaida Boko Haram Na Hulda Da 'Yan Ta'addan Waje


Gawarwakin mutanen da suka mutu a Damaturu a cikin jerin hare-haren baya-bayan nan da aka shirya kaiwa a lokaci daya

Mayakan kungiyar ba su wuce daruruwa ba, kuma ba su da wani kwakkwaran tsarin shugabanci

Gargadin da ake bayarwa game da yiwuwar ganin karin hare-hare daga kungiyar nan da aka fi sani da sunan Boko Haram a Najeriya, na sanya ‘yan Najeriya da ma ‘yan Afirka zama cikin dari-dari na yiwuwar yaduwar ayyukan ta’addanci na cikin gida. Kwararru a nan Amurka sun bayyana ‘yan tawayen na Boko Haram a zaman wadanda suke da wuyar bin sawu, wadanda kuma suke rarrabe. Wakilin Muryar Amurka, Nico Colombant, yace an kai hare-hare na baya-bayan nan kan ofisoshin ‘yan sanda, da majami’a da sansanin soja ran 4 ga watan nan na Nuwamba a wasu kananan garuruwa a arewacin Najeriya. An kashe mutane fiye da 100 a wannan lamarin da kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce shi ne mace-mace mafi muni cikin rana guda a kasar tun 2009. An dora laifin hare-haren a kan kungiyar Boko Haram, wadda ke nuna karin turjiya da karin kwarewa wajen kai hare-hare kan cibiyoyin da yawansu ke karuwa.

Amma kuma kwararru kan harkokin Afirka kamar su Peter Lewis, darektan sashen nazarin harkokin Afirka a Jami’ar John Hopkins, yace har yanzu kansa yana rude, bai fahimci alkiblar wannan kungiya ta Boko Haram ba. Ya ci gaba da cewa 'yan Boko haram sun nuna cewa zasu iya shirya kai manyan hare-hare, kuma sun iya tsara yadda wasu daga cikin wadannan hare-hare zasu gudana. Amma duk idan ka tara su, sai ka ga babu kan gado a tsarin dabarun wannan kungiya ta Boko Haram. Wai shin me ta ke nema ne a zahiri? Me suke kokarin yi ne? Amsar wadannan batutuwa ba a fili take ba.

Har yanzu, akwai abubuwa da dama da jama’a ba su sani ba game da ‘yan Boko Haram, wadanda suka shafe kusan shekaru 10 da bullowa a Najeriya. Masu magana da yawun kungiyar da yawa sun ce su na gwagwarmaya ce ta neman kafa kasa mai zaman kanta mai bin shari’ar Musulunci a arewacin Najeriya. An yi kiyasin cewa mayakan kungiyar ba su wuce daruruwa ba, kuma ba su da tsarin shugabanci guda mai karfi.

Tun shekarar 2009, ‘yan Boko Haram suke auna hare-hare a kan ‘yan sanda da sojojin Najeriya. Sun kai hare-hare kan gidajen kurkuku domin kwato membobinsu dake daure, suka kai hare-hare kan bankuna domin samo kudade, suka kuma kai wani mummunan harin bam a kan ofishin MDD na Najeriya a Abuja. Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce an kashe mutane fiye da 400 a hare-haren kungiyar cikin wannan shekara kawai.

Gwamnatin Najeriya ta mayarda martani ta hanyar kara girka sojoji a wasu sassan arewacin Najeriya inda kungiyar ta ke da karfi, a wasu lokuta ma sojojin su na daukar matakai masu tsauri kamar irin matakin da suka dauka na bi gida-gida su na neman makamai cikin makon da ya shige a garin Maiduguri. William Minter, editan wata mujallar da ake wallafawa ta Internet mai suna Africa Focus, yace irin matakan da gwamnatin ta ke dauka su na harzuka wasu mutane su na shiga cikin kungiyar ta Boko Haram. Sannan ya kara da cewa rahotannin kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun bayyana a fili cewa a lokacin da aka dauki matakan murkushe wannan kungiya a shekarar 2009, dakarun tsaro sun ci zarafin fararen hula masu yawa wadanda ba su san fari ba balle baki. Wannan abinda suka yi ya karawa kungiyar goyon bayan jama’a.

Taswirar kasar Najeriya da makwaftan ta irin su Nijer da Chadi da aka ce 'yan Boko Haram na shiga cikin sauki
Taswirar kasar Najeriya da makwaftan ta irin su Nijer da Chadi da aka ce 'yan Boko Haram na shiga cikin sauki

Shekarar ta 2009, tana da muhimmanci ga wannan tawaye dake faruwa a arewacin Najeriya. A shekarar ne, shugaban kungiyar Boko Haram Mohammed Yusuf ya kunno kai wajen tayar da kayar bayan da aka tura sojoji domin su murkushe. An yi kisan gilla ga wasu na hannun damar shi Muhammadu Yusuf da dama, yayin da shi ma kansa ya mutu a hannun ‘yan sanda. Akwai jami’an tsaron da aka ce da hannunsu wajen kashe shi da mukarraban nasa a lokacin. A cikin wannan shekarar, an gurfanar da jami’an ‘yan sanda guda biyar a gaban kotu ana tuhumarsu da kashe-kashen, kuma har yanzu wannan shari’a ta su tana gudana. John Campbell, tsohon jakadan Amurka ne a Najeriya wanda a yanzu yake Majalisar Hulda da Kasashen Waje ta Amurka. Yace irin wadannan matakan nuna karfi da isa na gwamnati babu abinda suke haifarwa illa su kara sa jama’a su na goyon baya da tausayawa ‘yan Boko Haram. John Campbell ya ci gaba da cewa ba ka bukatar mutane da yawa (idan kana son tayar da tawaye ko yin tawaye). Abinda kake bukata shi ne janyo ra’ayin jama’a su yarda cewa ba zasu tsoma baki cikin harkarka ba, (watau ba zasu fadawa hukuma wani abu game da kai ba).

A yanzu dai, shugaba Goodluck Jonathan yana bin dabarar yin amfani da dakarun tsaro ne wajen shawo kan wannan bore a bayan da shugabannin Boko Haram suka ki yarda su ajiye makamai su fara tattaunawa da hukuma. Amma kuma dakarun Najeriya su na da matsaloli masu yawa wajen farautar ‘yan kungiyar ta Boko Haram. Rashin tsarin shugabanci mai karfi da kuma yadda suke sajewa cikin jama’a sun sa hukumomi su na fuskantar wahala sosai wajen gano magoya bayan kungiyar. Masu fashin baki da masana suka ce ‘ya’yan kungiyar Boko Haram su na samun saukin shiga da fita a kasashe makwabta kamar Nijar da kamaru da kuma Chadi a saboda rashin tsaron iyaka da kuma goyon bayan da suke samu daga jama’ar yankin.

'Yan sandan Najeriya na sintiri akan tituna suna saka idanu
'Yan sandan Najeriya na sintiri akan tituna suna saka idanu

Haka kuma masu fashin baki da masana, sun ce babu wata kwakkwarar shaida har yanzu dake nuna cewa ‘yan Boko Haram su na da alaka da kungiyoyin ta’addanci a kusa da Najeriya ko a nesa da ita, duk da ikirarin da wasu da suka ce su ‘ya’yan kungiyar ne suke yi, da kuma gargadin da jami’an sojan Najeriya da na Amurka suke bayarwa game da haka.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG