Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Maganar Ta'addanci A Dalilan Faduwar Jirgin Rasha


Ma'aikatan ceto a kan teku
Ma'aikatan ceto a kan teku

A yau Litinin jami’an kasar Rasha sun bayyana cewa harin ta’addanci baya cikin abubuwan da suka sa Jirgin fasinjoji na sojin Rasha ya fadi inda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 92 da yake dauke dasu.

Mai Magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov yace “Ko kusa ta’addanci baya kusa da sanadi”.

Tun da farko a yau Litini din ne Ministan zirga-zirga Maxim Sokolov ya ce Hadarin jirgin na ranar lahadi ta iya yiwuwa ya farune sakamakon kuskuren Direban Jirgin ko kuma Matsalar inji.

Duk da dai ta’addanci baya cikin abinda ake zaton shi ne sanadin faduwar jirgin, Kwamitin bincike na musamman na Rasha ya kaddamar bincike na aikata laifi akan Hadarin.

Jirgin dai ya fada Kogin Bahar Aswad mintuna biyu bayan ya tashi daga filin jirgin sama na Sochi cikin yanayi mai kyau, inda ya yi sanadiyyar mutuwar ma’aikatan jirgin guda Takwas da kuma Fasinjoji 84, cikin su akwai mambobin sananniyar kungiyar mawakan sojojin Rasha na Red army da aka fi sani da Alexandrov Ensemble ko kuma Red Army Choir guda goma sha biyu.

XS
SM
MD
LG