shugaban kasar Vladimir Putin da Prime Minista Dmitry Medvedev da kuma ministan harkokin kasashen ketare Sergei Lavrov na daga cikin manyan baki da suka halarci bukin.
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan yace babu ko tantama, dan kungiyar limamin addinin Islama Fethullah Gulen ne yake da alhakin kisan gillan.
Yace babu bukatar boye boyen cewa, shi dan kungiyar FETO ne, sunan da ake kira kungiyar Fethullah Gulen.
A cikin hirarsu ta wayar tarho farkon wannan makon, ministan harkokin kasashen ketare na kasar Turkiya Mevlut Cavusoglu ya shaidawa sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry cewa, Turkiya ta hakikanta cewa, maharin yana da alaka da Gulen wanda yake zaune a Amurka, wanda ake kuma dorawa alhakin yunkurin juyin mulkin da aka yi a Turkiya cikin watan Yuli da bai yi nasara ba.