Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masar Ta Bukaci Dakatar Da Kada Kuri'a Kan Gine-ginen Isra'ila -MDD


Shugaban kasar masar Abdel Fatah Al sisi, REUTERS/Charles Platiau (FRANCE - Tags: POLITICS HEADSHOT) - RTR4FOAF

Jiya Alhamis Masar ta roki Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta dakatar da kuri'a da ake shirin yi kan kuduri da zai bukaci Is'raila ta tsayarda duk ayyukan gine gine a duk sansanonin 'yan share wuri zauna "har sai Illa masha'Allahu" a yankunan Falasdinawa.

Da kwamitin sulhun ya shirya zama jiya Alhamis domin a kada kuri'a kan kudurin, wadda ya bukaci a tsaida duk ayyukan gine gine a yankunan Falasdinawa, an kira matakin a zaman na muhimmi domin ceto "shirin kafa kasar Falasdinu wacce zata yi kafada da kafada da Isra'ila, a zama na lumana.

Haka nan kudurin yace sansanonin na yanzu, basu da "tasiri a dokance", kuma kasancewarsu "mummunar keta dokar kasa da kasa ce."

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump da kuma Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sun yi kira ga gwamnatin shugaba Obama ta hau kujerar naki kan kudurin.

Amurka taki amincewa da irin wannan kuduri a shekara ta 2011, amma majiyoyi da dama sun gayawa tashar talabijin ta NBC cewa, Amurka ta shirya zata kauracewa kuri'ar ta jiya, kamin daga bisani aka dakatar d a shirin baki daya.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka taki ta fadi matasayarta idan da za'a kada kuri'ar, da aka tuntubeta bayan da aka dakatar da shirin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG