Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Wani Shiri Na Dawo Da SARS - Rundunar 'Yan Sanda


Sifeton 'yan sandan Najeriya, Umman Alkali Baba (Facebook/Nigeria Police)

Mba ya ce “an riga an rusa SARS, kuma ba za’a sake dawo da ita ba ta ko wace siga.”

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce babu wani shiri da ake yi na sake dawo da rusasshiyar runduna ta musamman ta yaki da miyagun laifuka da aka fi sani da SARS.

Wata sanarwa da kakakin rundunar Frank Mba ya fitar, ta ce ta yi wannan bayanin ne biyo bayan wasu rahotannin da ake bazawa, da ke cewa babban Sufeto Janar na ‘yan sanda Usman Alkali Abba ya ba da umarnin sake farfado da rundunar ta SARS.

Mba ya ce “an riga an rusa SARS, kuma ba za’a sake dawo da ita ba ta ko wace siga.”

To sai dai ya ce rundunar ta ‘yan sanda na kokarin yi wani tsarin aiki da zai maye gurbin rundunar ta SARS da aka rusa, a fafutukar da ake yi na sake fasali da inganta ayukan ‘yan sanda a Najeriya.

Hakan ko na da manufar samawa ‘yan Najeriya sahihin tsarin aikin ‘yan sanda mai tattare da fasahar zamani da bin doka da oda.

Akan haka sanarwar ta yi kira ga al’umma da su yi watsi da rahotannin da ake bazawa, domin kuwa na kanzon kurege ne da ba su da tushe balle makama.

Masu Zanga-Zangar Sai An Soke Rundunar SARS a Abuja
Masu Zanga-Zangar Sai An Soke Rundunar SARS a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Najeriyar dai ta rusa rundunar ta yaki da fashi da makami da manyan laifuka ta SARS, biyo bayan wata gagarumar zanga-zanga ta nuna kin jinin rundunar a duk fadin kasar.

Bayan daukar matakin ne kuma, Sufeto Janar na wancan lokacin Mohammed Adamu ya ba da umarnin sake wuraren aiki ga dukkan jami’an rundunar ta SARS da aka rusa.

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG