Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ne Zai Bayyana Matsaya Ta Karshe Kan Makomar Abba Kyari - Dingyadi


DCP Abba Kyari (Instagram/Abba Kyari)
DCP Abba Kyari (Instagram/Abba Kyari)

A cewar ministan, hukumomin tsaro sun kammala bincikensu kuma tuni sun mika shawarwari da suka bayar ga hukumomin da ya kamata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne zai yanke matsaya ta karshe kan matakin da za'a dauka a kan DCP Abba Kyari, da wata kotun kasar Amurka ta bukaci a kamo mata shi, bisa tuhumarsa da alaka da Hushpuppi.

Ministan Lamurran 'Yan sandan Najeriya Muhammadu Maigari Dingyadi ya ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ne zai yi matsaya ta karshe dangane da lamarin DCP Abba Kyari, tsohon shugaban runduna ta musamman ta yaki da aikata miyagun laifuka ta 'yan sanda.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar talabijin ta Channels, Dingyadi ya ce gwamnatin Najeriya na bukatar ganin an yi duk abin da ya kamata akan lamarin Abba Kyari, kasancewar yana da alaka da matakin kasa-da-kasa.

Ministan Lamurran 'yan Sanda Muhammadu Maigari Dingyadi
Ministan Lamurran 'yan Sanda Muhammadu Maigari Dingyadi

Ya ce kamar yadda kowa ya sani ne rundunar 'yan sandan kasar ta kafa wani kwamiti domin yin cikakken bincike akan dukkan zarge-zargen da ake yi wa Kyari, kuma tuni da kwamitin ya kammala aikinsa tare da mika rahotonsa ga babban Sufeto Janar na 'yan sanda.

Ministan ya ce haka kuma an gabatar da rahoton kwamitin da shawarwarin da ya bayar ga ministan shari'a na kasa domin jin ra'ayinsa, a yayin da kuma ita ma ma'aikatar harkokin kasashen waje, za'a gabatar mata da rahoton, kafin daukar mataki na karshe akan lamarin.

"Abin da ya kamata 'yan Najeriya su sani shi ne, hukumomin 'yan sanda sun yi na su aiki kamar yadda ya kamata, kuma a bayyane suka gudanar da komai. Abin da ya rage yanzu shi ne shugaba Muhammadu Buhari ne zai yanke shawarar matakin da za'a dauka akan lamarin," in ji Maigari Dingyadi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Facebook/ Muhammadu Buhari)

Rundunar 'yan sandan kasar dai ta dakatar da Abba Kyari daga mukaminsa tare da maye gurbinsa, biyo bayan zarginsa da alaka kan badakalar zambar kudi ta yanar gizo da ake yi wa wani dan Najeriaya Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi a kasar Amurka.

Abba Kyari, hagu da Abbas Hushpuppi, dama (Instagram/ Abba Kyari/Hushpuppi
Abba Kyari, hagu da Abbas Hushpuppi, dama (Instagram/ Abba Kyari/Hushpuppi

Alkalin wata kotu a jihar California ta kasar Amurka, Otis Wright, ya baiwa hukumar binciken Amurka ta FBI umarnin kamo Abba Kyari da kuma gurfanar da shi a gaban ta a can kasar ta Amurka, domin amsa tuhumar da ake yi masa.

XS
SM
MD
LG