Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Babu Wata Tattaunawa Da Za A Yi Da Rwanda Muddin Tana Mamaye Da Wani Yankinmu" – Shugaban Kasar Congo


Shugaban kasar Congo Félix Tshisekedi
Shugaban kasar Congo Félix Tshisekedi

Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 12 a wasu hare-hare da aka kai a wani yankin karkara a gabashin Congo, wani jami’in yankin da kuma shugaban kungiyoyin farar hula suka ce, yayin da shugaban kasar Tshisekedi, ya yi watsi da tattaunawa da makwabciyarta Rwanda kan wani rikici makamancin wannan

WASHINGTON, D. C. - Kisan da aka yi a lardin Arewacin Kivu na Congo ya faru ne a ranar Talatar da ta gabata, kuma dakarun Allied Democratic Forces ne suka aikata, mayakan da ake kyautata zaton suna da alaka da kungiyar IS mai tsatsauran ra'ayi.

Rikici a Congo
Rikici a Congo

‘Yan ta’addan sun kai hari a kauyuka uku a yankin Beni, a cewar Kinos Katuho, shugaban kungiyar farar hula ta Mamove.

Gabashin Congo ya kwashe shekaru da dama yana fama da tashe-tashen hankula da makami, yayin da kungiyoyi sama da 120 ke fafutukar neman mulki, filaye da albarkatun ma'adinai masu mahimmanci, yayin da kuma wasu ke kokarin kare al'ummominsu.

Kungiyoyin da ke dauke da makamai sun dade suna gudanar da yakin neman zabe a yankin mai arzikin ma'adinai kuma ana zarginsu da kisan gilla.

Rikicin ya barke ne tun a karshen shekarar 2021, lokacin da wata kungiyar 'yan tawaye, mai suna M23, wadda ta kasance a boye, ta sake kunno kai tare da fara kai hare-hare domin kwace yankuna. Ana zargin kungiyar na samun goyon baya daga makwabciyar kasar Rwanda, ko da yake kasar ta musanta haka.

A halin da ake ciki, shugaban kasar Congo Félix Tshisekedi a ranar Talata ya sake nanata ikirarin da ya yi cewa 'yan tawayen M23 na samun goyon baya daga Rwanda, kuma ya ce ba zai shiga tattaunawa da shugaban Rwanda Paul Kagame ba kan wannan batu.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama suma sun ce mayakan na samun goyon baya ne daga kasar Rwanda.

Tshisekedi ya ce, "Babu wata tattaunawa da za a yi da maharan muddin sun mamaye wani yanki na yankinmu," in ji Tshisekedi, yayin da yake magana kan Rwanda a wata ganawa da jami'an diflomasiyya a Kinshasa babban birnin Congo.

"Babu wani sasantawa da za mu yi," in ji shi

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG