Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bai Halarta Kwararren Dan Jarida Ya Yada Labaran Da Bai Tantance Ba-NBC


Hukumar Kula da Kafofin Yada labarai ta Najeriya NBC
Hukumar Kula da Kafofin Yada labarai ta Najeriya NBC

A yayin tashar talabijan Arise TV ta nemi afuwa game da yada labarin karya kan Tinubu, Shugaban hukumar NBC, Balarabe Ilellah, ya ce NBC ta dauki wannan matakin ne don ya zama jan kunne ga sauran kafafen yada labarai.

Hukumar NBC din ta bayyana matakin da ta dauka na cin tarar gidan talabijin din Arise da ke zaman kanta a kasar kan Naira miliyan 2 a matsayin jan kunne ga sauran gidajen yada labarai a yayin yiwa muryar Amurka karin bayani a game da lamarin dake ci gaba da jawo marhaba da kuma suka a lokaci guda.

Hakan dai ya biyo bayan wani labarin karya da ake zargin gidan talabijin din ta yadawa akan dan takarar shugabancin Najeriya karkashin inuwar jam’iyya APC mai mulki, Asiwaju Ahmed Tinubu.

Tuni dai wasu 'yan Najeriya ke marhaba da wannan mataki na hukumar NBC inda wasu kuma ke kushewa tare da alakanta hakan da take hakkin 'yancin fadin albarkacin bakin dan Adam dake kunshe a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

A hirar shi da Muryar Amurka, Dakta Sule Yau Sule malami a tsangayar koyar da aikin jarida na jami’ar Bayero ta kano ya bayyana cewa, hakan ya yi daidai, duk wanda ya yi laifi lalle za a hukunta shi, domin ya zama izina ga kowanne gidan telebijin wanda ma zai so ya yi irin wannan abu.

Idan ana iya tunawa, gidan talabijin din Arise ya nemi afuwa a ranar Lahadin da ta gabata bayan da kamfannin ya yada rahoton cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC na binciken dan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, kan zargin karkatar da wasu kudade bayan aikata laifukan da suka shafi safarar miyagun kwayoyi.

Gabanni fara yakin neman zaben jam’iyyu a Najeriya na 2023, hukumar NBC ta fitar da tsare-tsare da ka’idoji ga kafofin yada labarai a wani mataki na kiyaye yada labarai da ka iya janyo tashin hakanli a lokutan yakin neman zabe a Najeriya.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da hukumar NBC ke kakabawa wani gidan talabijan tara sakamakon yada labaran kanzon kurege a kasar.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

XS
SM
MD
LG