Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bai Kamata Amnesty International Ta Zargi Sojan Najeriya Ba – inji Janar Yakubu Gawon


Sojojin da ake zargi da kin zuwa Arewa maso gabacin kasar domin yakar masu tsassauran ra'ayin addini sun hallara a gaba kotun Soja a Abuja, 2 ga Oktoba 2014.

A lokacin da Janar Yakubu Gawon yake magana a gurin taron da kwalejin tsaro ta Najeriya dake birnin Abuja ta shirya, domin hafsoshin dake halartar kwas na ashirin da hudu, yace ko kadan Amnesty Intertional bai kamata ta zargi sojojin Najeriya da yin kisa ga fararen hula ba, domin Boko Haram suke aikata abinda ake tsammanin sojan da aikatawa.

Janar Yakubu Gawon yace, “su zargi sojan Najeriya wannan ba dai dai bane, domin ba’a taba horas da sojan Najeriya suyi hakan ba, bai kamata suyi wannan zargi ba, wannan ba dai dai bane don haka su neman gafarar rundunar sojan Najeriya, dama Najeriyar.”

A nasa bangaren babban hafsan Najeriya, laftanar Janaral Tukur Buritai, yace kwanannan shugaban kasa ya amince da wasu kudade da za’a sayo wasu karin manyan makamai, ya kuma ce cikin wa’adin watanni ukun da aka baiwa sojan Najeriya su kawo karshen ‘yan Boko Haram, ya zuwa yanzu anyi nisa sosai kuma za’a cimma wa’adin kafin ma lokacin ya kare.

Tunda farko dai sai da sakatare da dindindin na ma’aikatar tsaron Najeriya, Isma’ila Aliyu yace, “Alamu duk sun tabbatar da za’a cimma wa’adin kawo karshen ‘yan Boko Haram, kamar yadda shugaban kasa yake da muradi.”

Saurari Cikakken Rahotan

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG