Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Kimanin Mutane 50


'Yan Bindiga

'Yan bindiga sun kashe Hakimin garin dama shugaban ‘yan Sandan

Wasu mahara dauke da manyan bindigogi sun kai hari tare da kashe mutane dea dama a yakin Alawa, dake cikin karamar hukumar Shiroro, ta jahar Neja a Najeriya.

Lamarin da ya faru a daren Talatan nan shaidun gani da ido sun ce har izuwa wayewar garin Laraban nan maharani suyi ta kona gidajen jama’a, tare da kashe dabbobin su akwai wahalar samun cikakken bayani saboda karancin hanyoyin sadarwa a yankin.

Amma bayanai sun ce maharan sun kashe kimanin mutane hamsin a ciki har da Hakimin garin na Alawa, dama shugaban ‘yan Sandan garin.

Gwamnatin jahar Neja, dai ta ce ta samu labarin afkuwar wannan lamari, sakataren yadda labarai na Gwamnan jahar Dr, Ibraheem Dooba, y ace lamarin abun tayar da hankali ne am sun sanarda jami’an tsaro.

Rundunar ‘yan Sandan jahar dai ta tabbatar da afkuwar wannan lamari, ta bakin kakakin rundunar ASP, Bala Elkana. Wannan al’amari dai yana zuwa ne a dai dai lokacin da aka kara tsaurara tsaro a jahar domin tukarar bukukuwan babban Sallah.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG