Accessibility links

A karo na farko, wata na’urar jigilar sararin sama da dan adam ya kirkiro ta iya ficewa daga zangon duniyoyin da ke dogaro ga rana, da ake kira solar system

A karo na farko, wata na’urar jigilar sararin sama da dan adam ya kirkiro ta iya ficewa daga zangon duniyoyin da ke dogaro ga rana, da ake kira solar system, ta shiga can cikin zangon sararin sama mai sanyi na “interstellar space.”

Hukumar Balaguro da binciken yanayin sararin sama ta Amurka, NASA a takaice, ta tabbatar jiya Alhamis cewa kunbon mai suna Voyager 1 Space Probe, wanda aka kaddamar cikin shekarar 1977, na wuri mai nisan kilomita miliyan dubu 19 daga rana kuma har ya kutsa cikin wani zangon sararin saman da ba a taba zuwa ba kuma wanda ba a san yanayinsa ba.

Hukumar ta NASA ta ce kunbon Voyager ya ketara can cikin wani zangon sararin subahana a bara, to amma hujjojin faruwar hakan ba su iso duniya ba sai zuwa tsawon wannan lokacin.

Hukumar ta NASA ta bayyana wannan al’amarin da cewa shi ne mafiyin cigaban fasaha a daukacin tarihin kimiyya.

A yanzu na’urar kunbon Voyager za ta binciki wasu sassan sararin saman da ba a taba bincika ba. Idan komai ya wakana yadda aka tsara, na’urar kunbon Voyager za ta rinka turo bayanan abubuwan da ta gano zuwa duniya har zuwa shekara ta 2025, lokacin da ake kyautata zaton makamashin nukiliyar da ta ke amfani da shi zai kare.
XS
SM
MD
LG