Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bama Bamai Sun Kashe Mutane Tara a Kasar Libya a Jiya Talata


Wani Mutum a inda Bama Bamai suka pashe
Wani Mutum a inda Bama Bamai suka pashe

Wasu tagwayen bam baman cikin mota da suka tsahi sun kashe mutane akalla tara kana kuma suka jikata sama da wasu 30 a Benghazi na kasar Libya a jiya Talata.

Mota guda ta tarwatse ne a wajen wani masallacin dake unguwar al-Salmani. Jim kadan bayan minti 30 kuma mota ta biyu ta abkwa yan sanda da masu aikin ceto dake kwasan mutanen da suka jikata a harin na farko.

Ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin.

Benghazi itace cibiyar da aka gwabza mummunar fada tsakanin masu tsattsaurar ra’ayi da rundunar masu biyayya ga jarumin sojan Libya Khalifa Haftar. Ya ayyana birnin mai cin gashin kansa a bara.

Libya ta fada cikin tashe tashen hankula na lokaci mai tsawo tun bayan da aka hambarar kuma aka kashe tsohon shugaban kama karya Moammar Gadhafi a shekarar 2011.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG