Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bamabamai Biyar Suka Tashi a Zirin Gaza Yau Da Safe


 Marwan Shtewi, 32,daya daga cikin wadanda suka ji ciwo a tashin bamabaman
Marwan Shtewi, 32,daya daga cikin wadanda suka ji ciwo a tashin bamabaman

Bamabamai biyar da suka tashi a zirin Gaza sun hallaka mutum daya amma mutane da dama ne suka jikata

Bamai bamai akalla guda biyar ne suka tashi da sanyin safiyar yau Alhamis a Zirin Gaza. Ana kuma kyautata zaton mutum daya yaji rauni a sakamakon tashin bama baman.

Wakiliyar Muryar Amurka a yankin Heather Murdock tace taji tashin bama baman kuma ana jin karan motocin daukan mara lafiya akan tituna jim kadan bayan tashin bama baman.

Mazauna yankin sunce suna kyautata zaton an auna harin bama baman akan sansanonin yan kungiyar Hamas.

Wannan alamari ya faru ne bayan zanga zangar da aka yi a wannan makon akan iyakar Gaza da Isira’ila. Fye da mutane sittin suka mutu fiye da dubu biyu da dari bakwai kuma suka ji rauni. Jiya Laraba jami’in Hamas da aka yi hira da shi, ya ce hamsin daga ciki wadanda aka kashe yan kungiyar Hamas ne. Saura mutum goma sha biyu farar hula ne. Yace daga cikin wadanda aka kashe akwai mata da yara da wata jaririyar yar watani takwas da haihuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG