Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zangar Falasdinawa Ya Kazance A Yayin Da Amurka Ta Bude Ofishin Jakadancinta A Birnin Kudus


Diyar Shugaba Trump, Ivanka Trump da sauran jama'a a yayin da ake kaddamar da Ofishin Jakadancin Amurka.
Diyar Shugaba Trump, Ivanka Trump da sauran jama'a a yayin da ake kaddamar da Ofishin Jakadancin Amurka.

Ma’aikatar lafiyar Gaza ta bayyana cewa dakarun Israila sun harbe a kalla Falasdinawa 16 har lahira akan iyakar Gaza inda dubban mutane suka hadu domin yin zanga-zanga kan shirye shiryen da Amurka ke yin na dauke ofishin jakadancin ta daga Tel Aviv da maida shi Kudus.

Ma’aikatan lafiyar ta ce a kalla mutane 500 ne suka raunana daga harbin bindiga. Mace-macen ya kara yawan Falasdinawan da sojojin Isra’ila suka kashe a cikin makonni shida da suke ta zanga zanga zuwa fiye da mutane 50.

Masu sharhi sun zargi Israila da bude wutar da sukayi, inda su kuma sojojin Yahudawan suka ce hakan ya zama tilas saboda tsaro, domin mutanen na kawo barazana ga shingen kan iyakar.

Masu zanga zangar sun jefa abubuwa da dama ta kan iyakar kuma sun kona tayoyi a gaban ofishin jkadancin da aka bude a yau din. An rufe Wuraren san’a da makarantu da dama a garin na Gaza.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG