Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bamabamai Sun Kashe Mutane Shida A Mogadishu Kasar Somali


Wurin da bamabamai suka tarwatse a Somalia
Wurin da bamabamai suka tarwatse a Somalia

Bamabaman da suka tashi jiya Lahadi a Mogadishu babban birnin Somalia sun hallaka mutane shida tare da jikata wasu

Wasu bama-bamai biyu da aka boye cikin motoci biyu, aka tada dasu a birnin Mogadishu babban birnin Somalia, sun kashe mutane shida, kana wasu biyar suka jikkata a jiya Lahadi, a cewar wasu shaidungani da ido.


Mota daya dake dauke da bam din ta tarwatse ne a wani babban shingen-duba motoci a Mogadishu, ta kashe mutane hudu kana ta raunata akalla wasu mutanen kuma hudu, kamar yadda ma'aikatan kiwon lafiya suka yi bayani.


Wasu shedun gani da ido sun ce, daya motar da dan kunar bakin wake yake tukawa ya karata a wani wurin duba ababan hawa lokacind a ya taho da gudu, bayan soja ya bukaci da ya tsaya.Nan take ya kashe sojan, kamar yadda shedun suka yi bayani.


Bam din ya kashe wasu fararen hula da suke tsaye a gefe da kuma maharin.

A cikin wani harin kunar bakin wake kuma da aka kaiwa masallacin yan darikar Shi’a a birnin Herat dake gabashin Afgahanistan, dake kan iyakar kasar da Iran, ya kashe akalla mutum guda kana kuma ya raunata wasu mutane tara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG