Accessibility links

Bamanga Tukur ne sanadiyar rigin-gimun da suka addabi jami'yyar PDP?

Rikicin jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya ya ki ci kuma ya ki cinyewa. Ana zaton shugaban jam'iyyar Alhaji Bamanga Tukur shi ne umal-uba-isan rigin-gimun.

Domin samo tushen rigin-gimun manyan jami'an jam'iyyar basa so su fadi dalilin rikicin nasu.Bisa ga wasu alamu gwamnatin kasar tana matsawa Alhaji Bamanga Tukur da ya yi murabus daga mukaminsa. To sai dai manyan jami'an PDP suna kaucewa duk wata tambaya a kan matsawar da gwamnati ke yiwa Bamanga ya yi murabus. Gwamnatin na bukatar ya yi murabus domin farantawa wasu gwamnonin PDP da suke barazanar janye goyon bayansu daga shugaba Jonathan su kuma bar jam'iyyar gaba daya.

Sabuwar jam'iyyar APC tana farin cikin yadda Bamanga ke gudanar da harkokin jam'iyyar ta PDP. Sabuwar jam'iyyar na ganin yadda Bamanga ke gudanar da PDP ya rage masu wahalar fafitikar neman karbe madafin iko daga ita PDP a shekarar 2015. Wasu ma na alwashin akwai gimshikan PDP da dama da zasu shiga sabuwar jam'iyyar. Yin hakan zai kara wa tungar adawa tagomashi.

Faruk Adamu Aliyu ya tabbatar cewa suna da baragurbin yan PDP dake masu aiki. Ya ce shugaban PDP na kasa jam'iyyarsu ta APC ya ke yiwa aiki kuma suna murna da abubuwan da yake yi ya karasa jam'iyyar. Akwai wasu gwamnoni ma wadanda ya yi alkawarin bayyana sunayensu nan da mako daya da zasu shiga sabuwar jam'iyyar, har ma da 'yan majalisu.

An ce shugaba Jonathan ko ya ji a jikinsa kamar yadda Nasiru Zaharadeen mai kula da harkar jama'a ma shugaba Jonathan ya fada. Ya ce shugaban ba zai hana kowa yin abun da ya ke son ya yi ba. To sai dai ya musanta abubuwan da Alhaji Faruk Adamu Aliyu ya fada. Ya ce Gwamna Sule Lamido shi ne kan gaban masu sukar abubuwan dake faruwa a PDP to amma ya fito fili ya ce shi ba zai bar jam'iyyarsa ba zuwa wata sabuwa.

Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG