Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Furucin Dan Majalisar Dattawa Lawal Kan Jam'iyyun APC Da PDP


APC logo
APC logo

Dan Majalisar Dattawan Najeriya ya yi furuci kan `hadewar wasu jam'iyyu suka zama APC da babbar abokiyar hamayyarsu ta PDP.

Dan Dattawa Lawal ya soma furucinsa ne da bayyana banbancin abun da suka so yi a shekarar 2011 da wanda suka yi a wannan shekarar ta 2013.

A wanjan karon kawance suka so su yi kamar aure amma ba hadewa ba. A wancan lokacin kowace jama'iyya zata cigaba da zama yadda take sai dai kawance domin takarar zaben shugaban kasa. Amma a wannan lokacin kowa ya yadda a rushe jam'iyyarsa a dama a dunkule a zama daya a cikin sabuwar jam'iyyar APC.

Abokin aiki Aliyu Mustapha da ya zanta da Sanato Lawal ya ce mutane na ganin caca suka yi a ce manyan jam'iyyu sun rushe kansu sun dunkule su zama daya. Ya tambayeshi baya ganin shiga kwando daya kamar kasada suka yi. Sai Sanato ya ce ita rayuwa sai an hada da irin wannan cacar. Amma idan irin wannan cacar ta kama a yi sai a yi kuma da yadda Ubangiji abun da ake hangowa sai a cimmasa.

Dangane da cewa da can baya sun samu rabuwar kawuna domin raba mukamai da yadda za'a kashe kudade to ko wane shiri suka yi yanzu su kauce ma sake aukuwar wannan lamarin? Sanato Lawal ya ce duk sun yadda cewa daga ranar da aka ce sun rushe jam'iyyunsu sun kuma samu ragista na sabuwar jam'iyya to kada wani ya sake tunanen jam'iyyarsa ta da. Yanzu duk zasu fara sabuwar tafiya ce. Game da cewa ko sun tsayar da dan takarar shugaban kasa sai ya ce a jam'iyyarsu ta APC basu taba tunanen wanene zai tsaya takarar shugaban kasa ba. Ya ce abun da suka sa gaba yanzu shi ne yadda zasu gina APC ta zama jam'iyya.

Game da cewa 'yan PDP sun ce jam'iyyarsu jaririya ce ko tafiya ma bata fara yi ba sai ya ce duk dan PDP da ya yi wannan furucin bai bashi mamaki ba domin duk dan siyasa baya irin wannan magana. Ya ce su ba sabuwar jam'iyya ba ce. Hadewa suka yi. Ya ce cikin PDP ya duri ruwa kuma yanzu duk wani mataki da suka dauka sai sun yi kuskure.

Da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG