Accessibility links

Shugabannin APC na kasa da suka kama hanyar Gombe cikin jirgin sama domin su kaddamar da shugabannin jam'iyyar na jihar Gombe bai sanu sauka ba.

Rahotanni na cewa an hana jirgin saman da ya dauko shugabannin jam'iyyar adawa ta APC sauka a filin saukar jiragen sama dake garin Gombe.

Wakilan jam'iyyar su ne uwar jam'iyyar ta tura zuwa Gombe domin kaddamar da shugaban riko na jihar. Hamisu Mailantarki da kuma Dasuki Jalo Waziri sun yi karin bayani.Mailantarki ya ce sun shigo jirgi sun zo zasu sauka a ka fada masu cewa an tare filin saukar jiragen sama na Gombe don haka ba zasu iya sauka ba. Dalili ke nan suka koma Bauchi inda suka shigo motoci zuwa Gombe kodayake sun makara taron. Ya ce abun da ya faru yana da alaka da saiyasa.

Shi ma Dasuki Waziri ya ce daga Kano suka taso da jirgin kuma suna kokarin sauka aka ce mota ta baci a kan filin saukar jirgi don haka ba zasu iya sauka ba. Sai suka koma Bauchi suka sauka inda suka shigo motoci zuwa Gombe. Ya ce hakikanin gaskiya siyasa ce kawai.

Duk da matsalar da suka fuskanta an kaddamar da shugabannin rikon su guda biyar inda mataimakin shugaban jam'iyyar na arewa maso gabas Dr Umar Duhu ya yi bayani. Ya ce ya zo ne ya kaddamar da shugabannin riko na jam'iyyarsu ta APC reshen jihar Gombe.Barrister Mohammed Magaji Dohu shi ne mai kujera. Zai shugabanci mutane goma sha biyar da zasu rika jawo mutane cikin jam'iyyar a jihar Gombe bisa ga tsarin PDP.

Shugabannin riko ba sai an yi zabe ba . Su ne zasu rike jam'iyyar har ta habaka kana a yi zabe wanda za'a fara daga kananan hukumomi har zuwa tarayya.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG