Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bamanga Yace Zasu Ladaftar Da 'Yan Tawaye


Wani taron jam'iyyar PDP mai mulki a Nijeriya. Akan auna tarurrukan siyasa da bama-bamai a Nijeriya a 'yan kwanakin nan.
Wani taron jam'iyyar PDP mai mulki a Nijeriya. Akan auna tarurrukan siyasa da bama-bamai a Nijeriya a 'yan kwanakin nan.

Lokacin da yake mayarda martani game da darewar jam'iyyarsa Bamanga Tukur ya ce zasu ladaftar da 'yan tawayen

Tun ranar Asabar da wasu jigajigan PDP suka fice daga harabar taronsu na kasa da shailar kafa wata sabuwar PDP karkashin shugabancin Kawu Baraje bangaren Bamanga Tukur bai ce komi ba sai yau.

Yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai Alhaji Bamanga Tukur shugaban tsohuwar PDP ya ce zasu ladafta duk wadanda suka yi tawaye bisa ga dokokin jam'iyyar da na kasa. Ya ce babu wani bangaren jam'iyyarsa da ya balle. Kuma shi yana nan rike da ita daram. Ya ce zasu bukaci jami'an tsaro su yi diran mikiya kan duk wadanda suka ware daga garesu. Bamanga Tukur ya kara da cewa zasu sanar cewa sun ma sauka daga kujerunsu.

Sanato Abubakar Gada mai taimakon Bamanga Tukur ya ce sun dauki tsatsauran matakin ne domin 'yan tawayen sun karya doka kuma dole ne a ladaftar dasu. Ya ce kowane mukami mutum ke rike dashi ya sameshi ne karkashin jam'iyya, jam'iyya kuma ta fi kowa girma. Don haka duk wanda ya ja da jam'iyyar dole ya kuka da kansa.

Yanzu sai a sa ido a gani domin sabuwar PDP ta shigar da kara tana cewa a soke zaben da jam'iyyar ta yi makon jiya kana a kori Bamanga Tukur domin shi ba dan PDP ba ne. Da alama dai duk wata hanya ta sulhu ta rushe.

Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG