Wadansu ‘Yan bindiga da suke ikirarin wakiltar kungiyar hadaddun kungiyoyi a Yankin Niger Delta sun gudanar da wata zanga zanga yau a Birnin Fatakwal Jahar Rivers kan cewar, hukumar EFCC ta dena muzgunawa matar Tsohon Shugaban Kasa Patience Jonathan, ta wajen gundar binciken ba gaira ba dalili.
Masu zanga zangar mazansu da Matansu sun dunguma kan titunan Birnin na Fatakwal inda suka fara ziyartar Hedikwatar Yan Sandan Jahar da ke kan titin Moscow Road , daga nan kuma suka karkata zuwa Hedikwatar Ofishin Hukumar da ke yaki da yan yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC.
A cikin hirarshi da wakilin Sashen Hausa, shugaban Yan zanga zangar Ambassador Sukubo Sarai Sukubo yace sun fito zanga zanga yau ne, tare da zuwa Hukumar EFCC domin mika mata takardar koken cewar ba zasu lamunci yadda ake cin mutuncin Matar tsohon Shugaban Najeriya GoodLuck Jonathan ba. Bisa ga cewarshi, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta tashi haikan domin cin mutuncin Iyalan tsohon Shugaban, abinda yace ba zasu lamunta ba.
Da yake maida martani, Jamiin EFCC da ke zaman mukaddashin hukumar a Jahar ta Rivers Usman Muhamma Muktar, ya bayyana cewa, Hukumar ba zata yi kasa a guiwa ba wajen gudanar da ayyukanta.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu a yankin Niger Delta Lamido Abubakar ya aiko mana.