Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nazari Akan Ganawar Da Shugaban Najeriya Da Shugaban Amurka Zasu Yi Yau


Shugaba Buhari da Shugaba Trump
Shugaba Buhari da Shugaba Trump

Masana na ganin shugabanin biyu zasu tattauna akan abubuwa da yawa saboda Amurka na son kasancewa kan gaba cikin kasashen dake taimakawa Najeriya wajen yaki da ta’addanci, sai dai akwai bukatar Najeriya din ta yi taka tsantsan da wasu halayen kasashen yammacin Turai

Sha’anin tsaro na daga cikin babutuwan da zasu mamaye tattaunawa tsakanin Shugaba Muhammad Buhari na Nigeria da takwaran aikinsa na kasar Amurka, Donald Trump.

Manjo Janar Jinaidu Bindawa tsohon babban kwamandan rundunar sojojin Najeriya, yace za’a taba maganar tsaro zai kasance kan gaba, saboda ba Najeriya kadai ya shafa ba har da ma sauran kasashen Afirka da ma duniya ga baki dayan ta. Yadda rikicin Boko Haram ya ki ci ya ki cinyewa kuma gashi sun rabu suna bin wasu bangarorin kungiyoyin ‘yan ta’adda irinsu ISIS a duniya.

Maimakon ya zamana tashin hankalin na Najeriya kadai ne , yanzu ya hada da wasu kasashe, tamkar ma ya zama na duniya ne gaba daya.

Shi kuwa Malam Kabiru Adamu, masanin harkokin tsaro yayi hasashe akan akan abinda shugaba Amurka zai nema wajen shugaba Buhari. Yace idan ba’a manta ba Shugaba Trump ya yi alkawarin neman hada kan kasashe wurin yaki da ta’addanci, saboda haka yayi hasashen Shugaba Trump zai karfafa wa Najeriya gwiwa, ta dauki matakai kwarara fiye da na yanzu akan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Shi ko Wing Commander Isa Musa Salmanu cewa ya yi lallai Najeriya ka iya cin moriyar wannan ziyarar ta Shugaba Buhari saboda yanzu Amurka ta ga akwai ci gaba a yaki da ta’addanci dalili ke nan da ta kudiri anniyar sayarwa kasar jiragen yaki. Bugu da kari tana son ta kasance kan gaba cikin kasashen dake taimakawa Najeriya a yaki da ta’addanci.

Sai dai Janar Bindawa ya yi kashedi, cewa Amurka da kasashen yammacin Turai idan suka mika ma wani abu da hannun dama sai su yi anfani da hannun hagu su karbe. A cewarsa akwai abubuwa da yawa da zasu tattauna akai da zasu amfani Najeriya da sauran kasashen dake yaki da ta’addanci.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG