Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Ki-moon Ya Nemi A Gudanar Da Bincike Kan Harin Da Ya Kashe Mutane 30 A Syria


Ban Ki-moon

Babban Sakataren MDD Ban Ki-moon, ya nemi a gudanar da bincike mai zurfi kan wani harin jiragen sama da aka kai ran Larabar shekaranjiya kan wata makaranta dake Syria, inda har aka hallaka mutane kusan 30, galibinsu duk yara kanana.

Sanarwar da Babban Sakataren ya bada tace idan har aka tabattarda cewa wannan harin na ganganci, to ya tabatta laifin yaki.

Shima tsohon Fara Ministan Biritaniya Gordon Brown wanda shima manzon musamman ne na MDD kan sha’nin ilmi, ya nemi a yi wannan binciken.

Jiragen saman yaki ne suka kai hare-hare har guda shidda akan wani kauye dake yankin Idlib dake hannun ‘yantawaye, wanda a lokacin ne suka saki bam akan wannan makarantar inda suka hallaka malamai 6 da ‘yan-makarantar su 22, a cewar cibiyar adawar Syria ta “Observatory.”

Da ita cibiyar ta Observatory da fadar shugaban Amurka ta White House dai duk suna dora laifin kan harin ne a kan Rasha ko kuma Syria, amma kakakin ma’aikatar harakokin wajen Rasha, Igor Konashenkov, yace jiragen Rasha basu ratsa sararin wannan yankin a lokacinda aka kai farmakin ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG