Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin CBN Ya Sake Adadin Kudin Da Ake Biya a Hada Hadar Wayar Hannu Da Lataroni


Muhammadu Buhari

Babban bankin Najeriya (CBN) ya fito da wani sabon tsarin biyan kudi da masu amfani da wayar hannu ko konfuta za su rika yi a kan duk wata kira ko amfani da hanyar sadarwa karkashin yarjejeniyar ayyukan kamfanonin sadarwa (USSD).

Babban bankin ya sanar cewa daga yau Talata, kwastamomi za su biya N6.98 a kan kowace hada hada suka yi ta amfani da hanyar sadarwar.

Wannan sanarwa ta samu sanya hannu na hadin gwiwa tsakanin Mukaddashin Darektan Ayyukan Sadarwa na CBN, Osita Nwanisobi da kuma Darektan harkokin jama’a a Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), Ikechukwu Adinde.

Daga yau 16 ga watan Maris, 2021, hada hadar kudi da za a gudanar ta yarjejeniyar (USSD) a tsarin ajiyan kudi a banki ko a ma’aikatun kudi da bankin na CNB ya basu lasisin gudanar aiki, za a karbi N6.98 a kan kowace hada hada.

Wannan tsarin zai maye gurbin tsarin biyan kudi na kowane lokacin da aka yi amfani da waya, zai sa masu amfani da hanyar sadarwar su biya kudi mai rahusa, inji wani bangare na rahoton.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, wannan matakin zai fayyace komai zai kuma tabbatar da kudin biya bai karu ba koda sau nawa aka yi amfani da wayar a tsawon lokacin hada hada guda.

XS
SM
MD
LG