Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankunan Kasuwanci Zasu Mike A Najeriya: Dr Muktar


Wani dan canji a Najeriya
Wani dan canji a Najeriya

Wani masani a fannin tattalin arziki yace Bankunan kasuwanci zasu nemi hanyoyin rayuwa idan aka fara aiwatar da umarnin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari na ajia a banki daya.

A cikin hirarsu da Sashen Hausa, Dr Mustapha Muktar yace,wannan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na umartan gwamnatocin jihohi da ma’aikatun gwamnmatin tarayya su rika ajiye kudinsu a banki daya suna da alfano ta fannoni da dama. Na farko idan aka dubi kudaden gwamnati da suke yoyewa idan an karba kasancewa a da ana bude ajiya ne a bankunan kasuwanci da yawa, wani lokaci sai kudin ya yoye baije hannun gwamnati ba wannan zai sa aci amfanin kudin.

Yace wannan zai rage cin hanci da rashawa, banda haka kuma zai karawa gwamnati karfin guiwa ta iya gudanar da wadansu ayyuka da take gaza aiwatarwa sabili da kudaden basu shiga.

A bangaren cibiyoyin kasuwancin kuma Dr Murktar yace yanzu bankunan dake dogaro ga irin wannan ajiyar zasu tashi tsaye domin su nemi wadansu hanyoyin da zasu rayu. Yace ko da yake da farko zai iya zama babbar kalubala ga bankunan da ya yiwu da dama su nemi zaftare ma’aikata, amma daga baya zasu mike su rika gudanar da ayyuka yadda ya kamata bankunan kasuwanci su yi.

Cikakkiyar hirarsu da Mahmud Lalo

Ajiyar Kudin gwamnati a Najeriya:3:14"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG