Accessibility links

Baraka Ta Tabbata A Jam'iyar CDS Rahama Ta Kasar Nijer


Siyasar Nijer.

Wata kotun Niamey ta baiwa CDS Rahama bangaren Abdou Labo gaskiya a shari'ar da ta hada shi da bangaren tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane

Shari'ar ta wannan karo ta samo asali ne tun farkon barkewar rikicin jam'iyar CDS Rahama inda bangaren tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane ya shigar da kara a kotu da zummar kara nanata matsayin kwamitin kolin uwar jam'iyar game da maganar tsige wasu mataimakan shugaban ta su biyar wadanda su kuma suka tayar da kayar baya a kan matsayin da uwar jam'iyar ta dauka a shekarar 2011 na kin goyon bayan wani dan takarar shugaban kasar da ra'ayin shi ya sha bamban da na uwar jam'iyar ta CDS Rahama. Karshen dai rikicin ya kai jam'iyar CDS Rahama ga darewa gida biyu inda aka samu bangaren Mahamane Ousmane da kuma bangaren Abdou Labo. Bayan rabewar gida biyu bangaren Mahamane Ousmane ya kira wani babban taro a garin Damagaram inda ya tsige mataimakan shugaban duka biyar a shekarar da ta gabata, al'amarin da bangaren Abdou labo ya kalubalanta, kuma akan wannan batu ne wata kotu da ke birnin Niamey ta yanke hukuncin da ya baiwa bangaren Abdou Labo nasara a cikin watan yunin da ya gabata. Ga Sauran bayani daga bakin wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a birnin Niamey Abdoulaye Mamane Amadou.

XS
SM
MD
LG