Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barayi Ne Suka Kai Harin Ringim


Jami'an tsaro kenan ke sintiri a birnin Kano
Jami'an tsaro kenan ke sintiri a birnin Kano

Mukaddashin gwamnan Jihar Jigawa, Ahmed Mahmud, yace an nkashe mutane biyar a wannan harin da ya ce barayi ne suka kai shi, ba tsagera ba

Mataimakin gwamnan Jihar Jigawa, Ahmed Mahmud, yace hare-haren da suka haddasa mutuwar mutane akalla 5 daren lahadi a garin Ringim, barayi ne suka kai, babu wata nasaba da addini ko wata kungiyar addini.

A tattaunawar da yayi da Sashen Hausa na muryar Amurka, mataimakin gwamnan yace abubuwan da ya ganewa idanunsa da ya ziyarci wuraren da abin ya faru sun tabbatar masa da wannan hasashen, kuma ya kamanta wannan harin da wani wanda aka kai a garin Gwaram kwanakin baya.

Yace wadannan 'yan bindigar sun yi ta harbi a iska, suka kori mutanen gari, suka dasa bam karkashin wata mota jmai sulke ta 'yan sanda dake gadi a bakin kofar gidan tsohon sufeto-janar na 'yan sanda, Hafiz Ringim, suka kai farmaki kan ofishin 'yan sanda na garin, sannan suka killace suka kuma fasa bankin Unity.

Yace wadanda aka kashe su biyar sun hada da 'yan sanda uku da kuma masu gadi guda biyu na wannan banki.

Mukaddashin Gwamnan Jihar Jigawa Yana Maganar Harin Da Aka Kai Ringim - 2:53
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00
Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG