Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barazanar Tsige Gwamnan Ekiti Bai Yiwa PDP Dadi Ba


Shugaba Jonathan na PDP

'Yan majalisar dokokin jihar Ekiti su goma sha tara na jam'iyyar APC sun yi barazanar tsige gwamnan jihar Fayose.

Barazanar ta APC bata yiwa PDP dadi ba. Ta bukaci Janar Buhari ya shiga tsakani.

Sakataren labarun PDP Oliseh Metuh yace gwamna Al-Makura na jihar Nasarawa ya nemi taimakon shugabannin PDP wadanda suka taimaka masa ba'a tsigeshi ba. Saboda haka suna fatan PDP zata samu tukuici daga APC a wannan karon.

A wani bangaren kuma 'yan takaran gwamna na kara dagewa inda bayanai ke nuna cewa tsohon gwamnan Zamfara Mahmud Shinkafi da ya fadi bayan ya saba da maigidansa Yariman Bakura yake son dawowa a zaben ranar Asabar. Zai kara da gwamna Yari na APC.

Shinkafi yace a jiharsu akwai masu goyon bayan PDP da dama saboda haka da yaddar Ubangiji zai kai labari gida a zaben.

A Gombe ma tsohon gwamnan Sanata Haruna Goje yana kiran jama'a su zabi APC domn su kawar da gwamna mai ci yanzu Ibrahim Dankwambo na PDP. Yace gwamna Dankwambo mai cin amana ne. Ya ci tashi amanar kuma duk wadanda suka taimaka ya zama gwamna ya ci amanarsu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG